"Wannan rigima da ake Kano, ba rigimar Kano ba ce, rigima ce ta arewa, kuma ba rigimar arewa ba ce, rigima ce ta Najeriya, in ji Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya ce: "Saboda irin wadannan manyan mutane suna rigima, a ce ba wani wanda ya isa ya fito cikin dattijan arewa, irin sarakunanmu, Sarkin Musulmi da Sarkin Zazzau da Shehu Borno, manyan sarakunanmu da malamanmu..."
Rikicin ya shafi gididdiba masarautar Kano zuwa gida biyar tare da binciken fadar sarkin Kano da gwamnatin jihar ke yi a kan wasu biliyoyin kudaden da ake zargin masarautar ta kashe ba bisa ka'ida ba.
Bafarawa ya ce abin kunya ne a ce Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti, shi ne zai zo ya jagoranci sulhunta Sarkin Kano da gwamnan jihar.
Ya ce a ra'ayinsa maganar shugaban gwamnonin Najeriya (wanda Kayode Fayemi yake jagoranta) ba ta ma taso ba.
"Ai maganar karkashin kasa ba taso ba, tun da abu ya hito hili, ya kamata kowa a zo a ga mai ya ce," in ji Bafarawa.
A cewarsa: "Ina Sarkin Muslmi? Ina Sarkin Zazzau? Ina Shehun Borno? Wannan wata matafiya ce aka taba, wanda ya shafi wadannan mutane. Muna da mallamai, mallamai suna hakkin su zo su yi nasiha ga wadannan mutane."
Tsohon gwamnan ya ce kamata ya yi dattijan arewa su hadu a matsayin kwamiti wanda zai kunshi manyan mutane da malamai da masarautu da 'yan kasuwa.
"Shi ma kansa, uban tafiyar, ubanmu shugabanmu, Muhammadu Buhari, bai kamata ba ya zura ido ana wannan abu." a cewar fitaccen dan siyasar.
Bafarawa ya ce a yau idan Buhari ya kirawo su, ya tsawatar (magana ta mutu) ba sai ya sa kowa ba, "ubanmu ne, shugabanmu ne, shi as shugabanmu a arewa yau".
An tambayi Dalhatu Bafarawa wanda a lokacin mulkinsa ne aka nada Sarkin Musulmi Abubakar Sa'ad III, ko a ganinsa me ke kawo irin wannan rikici? Sai ya ce yana ganin shaidan ne.
®Bbchausa
©HausaLoaded
Post a Comment