Legit.ng ta tsakulo muku jerin matan 'manyan 'yan siyasa kyawawa guda hudu a kasar nan

A Najeriya shiga harkar siyasa ba karamin abu bane, domin siyasa a Najeriya abu ce mai hatsarin gaske, sai wadanda suka cika suka batse suke shiga harkar siyasa a Najeriya. Duk macen da ta auri dan siyasa a Najeriya ana yi mata kallon wacce Allah ya albarkaci rayuwarta, domin ana yi mata kallon wata mace ta dabanne.

Wannan karfin mulkin yana zama wani abu a garesu, domin nauyi yakan karu a kansu, domin sune suke da alhakin jagorantar mata wurin ganin an kawo cigaba ga al'umma.

Hakan ne yasa matsayin 'First Lady' yake da matukar muhimmanci. Ana bukatar mace mai kyau, mai ilimi, da basira. Hakan ne yasa zaku ga ba kowacce mace ke iya taka wannan matsayin ba.

Legit.ng ta tsakulo muku jerin matan 'manyan 'yan siyasa kyawawa guda hudu.

1. Precious Fani Kayode

Allah ya albarkace ta da kyakkyawar fata, ga kyau tamkar ita tayi kanta, bayan haka kuma Allah ya ba ta basira da ilimi.

Ta auri tsohon ministan jiragen sama, kuma babban dan siyasa a kasar nan, Femi Fani Kayode, Precious mai shekaru 30 tana da yara guda hudu, kuma har yanzu jikinta yana nan tamkar na yarinya.

A shekarar 2007, Precious ta lashe gasar macen da tafi kowacce kyau a Najeriya. Sannan kuma an zabeta ta wakilci Najeriya a taron kyawawan mata da aka yi a kasar Jamaica a shekarar 2014.


2. Aisha Bello Matawalle

Misis Aisha Matawalle, ita ce matar sabon gwamnan Zamfara na yanzu, kuma ta kasance kyakkyawar gaske, kuma 'yar boko, bayan rantsar da mijinta a matsayin gwamnan jihar Zamfara, maimakon ta zauna ta kwanta a gida, sai ta fito ita ma a dama da ita.

Da irin wannan kyakkyawar fuskar ta ta, kai da ganin ta kasan ta cika mai kyau kuma mai ilimi, ga ta da tausayin talaka musamman mata da yara kanana.

Aisha yanzu haka ta jajirce wurin ganin ta kawo sauyi na jin dadi ga al'ummar jihar ta.



3. Rashida Yahaya Bello

Da wannan kyakkyawar fuska irin ta ta, Hajiya Rashida Yahaya Bello mace ce da idan ta shigo daki duk duhunsa sai yayi haske.

Hajiya Rashida ita ma tace baza a bar ta a baya ba wurin ganin ta yiwa mutanen jihar ta Aiki. Zamanta tare da gwamnan jihar Kogi ba karamin kawo cigaba yayi ga al'ummar jihar ba.

Hajiya Rashida ta yiwa mutanen jihar Kogi ayyuka na alkhari tun kafin ta zamanto 'First Lady' a jihar.


4. lara Fortes Oshiomhole

Ta auri tsohon gwamnan jihar Edo kuma shugaban jam'iyyar APC na yanzu, Adams Oshiomhole, lara, ta yiwa garinsu nisa ba kadan ba, amma kuma kyakkyawa ce da kowanne mutum zai so ya ganta.

Mahaifinta dan kasar Cape Verden ne, mahaifiyar ta 'yar Najeriya, Fortes ta na da duk wata siffa na mace mai kyau.

lara ta yi aikin lauya, sannan ta yi aikin cikin jirgi, hakan ne ya bata ilimin zama 'First Lady' kuma shugabar mata ta jihar Edo.



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top