Lokuta da dama zamu kasance mu da iyalanmu da kuma yaranmu muna ta fama da ciwo a jiki da gamu a tareda maganin ciwon a cikin gidajenmu,amma sai mu je muna ta faman wahala wajen neman magani a wasu kasashe saboda rashin sanin cutukan da wadannan itatuwan suke magani
da kuma yanda ake sarrafa su a yi magani dasu

Gwanda kamar yanda muka sani, a na kiranta ga dukkanin Hausar Arewacin Nigeria,bishiya ce dake da tsayi wacce take da ganye launin kore(green leaves),tana haifuwar 'ya'ya manya wadanda keda zaki amma kuma zakin nasu bana sukari bane,natural sugar ne a tare da su.Ya'yan gwanda waton (fruits) suna kumshe da dimbin sinadirrai masu matukar amfanar jiki (essential vitamins and minerals )

Ganyen gwanda na ha6aka garkuwar jikin dan adam.Su dai garkuwar jiki waton (immunity) sune ke zama a  matsayin sojojin dake yaki da abokan gaba waton suna yaki da kwayoyin cuta a jiki,dan haka idan suka karamta ko su kayi rauni to a hakika jikin dan adam zai raggwanta kuma zai iya fuskantar barazanar kamuwa da cutuka daban daban.A dalili da haka akoi bukatar jikin dan adam ya samu garkuwar jiki masu karfin gaske dan su iya baiwa jiki kariya daga abokan gaba.Domin samun wannan damar to sai a lazimci amfani da tsirran itatuwan da kimiyya ta bada tabbacin cewa suna boosting na immunity ciki harda gwanda.

Ganyen gwanda na kashe cutukan fata sanadin samun sinadirin karapain a cikinsa wanda wannan keda tasirin kawarda fungal infections.

Ganyen gwanda na maganin gyambon ciki (ulcers) sai a nemo ganyen gwanda a wanke a shanya idan ya sha iska sai a sa6e a sanya ruwan dumi masu kyau a misalin rabin cup madaidaici sai a tarfa zuma kadan a sha da safe kullum bayan an karya.

Ganyen gwanda na kashin tsutsotsin ciki (intestinal worms)

Ganyen gwanda na maganin ciwon ga6o6in jiki da jiyojin jikin dan adam sabili da samuwar sinadirin chymopapain.

Ganyen gwanda na warkarda cutukan ciki da kumburin ciki da matsalolin da suka shafi na hanjin ciki.

Ganyen gwanda na wanke kazamta da wani abu mai cutarwa da yaiyi laulayi a kan babbar hanzanya.(cleanse colon from toxins)

Ganyen gwanda a binciken wani masani dake a kasar Japan mai suna  Dr.Nam Dang da shi da abokan aikinsa sun tabbatar da cewa ganyen gwanda na daukeda wasu sinadiran dake kashin kwayar cutar ciwon daji(cancer cells).Baya ga haka,shi kuma Gajowik A,et al a bincikensa ya gano wani sinadiri (lycopene) mai kashe kwayar cutar ciwon daji a dan haka ganyen gwanda na maganin ciwon daji.

Diyan gwanda (seeds) nasu na kara lafiyar zuciya dan samuwar vitamin A,C da E a cikinsa masu taimakon kare afkuwar matsaloli kamar su ciwon suga dana hanyoyin jini har zuwa gana zuciya.

Ganyen gwanda nada sinadiran papain da chymopapian masu rage kumburi a sassa da dama na jikin dan adam a binciken Molecular Nutrition and Food Research.

Ganyen gwanda na sanya laushin bayn gari idan ya yi tauri da yawa kamar na dabbobi(constipation).

Ganyen gwanda na narkarda sinadiran cholesterol da yawansu a jiki illa ne matuka musamman ga zuciya,vitamin E da C dake a ciki suna taimakawa dan hana kitsen daskarewa akan hanyoyin jini.
Ganyen gwanda na maganin basir mai tsiro da gudawa.

Ganyen gwanda na maganin kornafi.

Ganyen gwanda na maganin malaria a sanadin sinadirin Acetogenin dake a cikinsa.

Ganyen gwanda na maganin ciwon hanta.

Gargadi

kada mai juna biyu tayi amfani da ganyen gwanda domin yana motsa mahaifa.

Yawan shan ruwan ganyen gwaiba na haifarda ko dai ganin juyuwa ko zafin ciki da makamantansu a dan haka sai a san yanda za a sha.
Ka guji zama likitan kanka.Ilmin da ba naka ba sai kayi kokari ka neme shi ga wadanda suke da shi dan ita lafiya kiwonta ake yi.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top