An bayyana Malam Bahaushe a matsayin wani mutum wanda yake tozartawa gami da cin zarafin Mata da sunan aure, a tsakanin sauran jinsinan jama’ar kasar nan gaba daya.
Shugabar cibiyar ARRIDAH Foundation dake Kaduna Hajiya Rabi Salisu Ibrahim ta bayyana hakan, lokacin wata tattaunawa da wakilinmu da tayi dangane da batun dokar haramta karin aure da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya gabatar a birnin Kano.

Hajiya Rabi Ibrahim ta cigaba da cewar, babban abin mamaki ya kare akan Malam Bahaushe, wanda shi a rayuwarshi babu abinda ya tsare illa batun aure-aure, ya tara Mata hudu a gidan haya cikin talauci, yayin da iyali sukayi yawa a fara ina za’a saka dasu, karshen lamari a tattarasu a mikama wani Malamin allo da sunan almajiranci, batun tarbiyarsu kuwa ko oho.
Shugabar cibiyar ta Arridah tace lallai ne ya zama wajibi ga dukkanin wani mai hankali daya goyi da bayan wannan kuduri da mai martaba sarkin kano ya bijiro dashi na haramta karin aure akan Hausawa matalauta, domin shine zai kara tabbatar da daraja da kare kimar mata a kasar hausa, wadanda aka daukesu tamkar wasu kayan sawa, kasa lokacin da kake bukata, ka ciresu kuma lokacin da kake bukata.

Hajiya Rabi ta kuma soki lamirin wani hadisi na hausawa dake cewar wai bakin da Allah ya tsaga baya hana mishi abinci, inda tace wannan kalami na hausawa ya ci karo da tsari na rayuwa, domin babu inda Allah yace kaje ka dauko nauyin da baza ka iya saukewa ba, inda ta kara shawartar al’ummar hausawa dasu guji kawo tarnaki da cikas a duk lokacin da aka bijiro da wani batu na cigaba, musanman akan abinda ya shafi cigaban mata.

Hajiya Rabi ta kuma soki lamirin rubuce-rubucen da wasu hausawa masu adawa da batun Sarkin Kano sukeyi a kafafen sadarwa na zamani, inda suke fadin cewar wai da zina cikin wadata gwamma aure cikin talauci, inda ta bayyana cewar wannan magana ba gaskiya bane, domin mata da dama kamar zawarawa dama wasu ‘yan matan talauci na jefasu cikin wani hali na kauce hanya na zinar talauci, ashe ya dace mu fahimci hikima ta mai martaba sarki akan wannan batu daya kawo, kasancewarshi mai digirin digirgir a fannin shari’ar musulunci.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top