Babban jam'iyyar adawa ta kungiyar yan'uwa musulmi dake fadin Masar na zanga-zangar nuna adawa da shakku kan kisan tsohon shugaban kasar wanda sojoji suka hambarar Muhammad Mursi.

Ba iya ýaýan Kungiyan ikwan ce suke zanga zangar ba ciki har da Al'umman Kasar, masoya da waɗanda suke kallon abin da gwamnatin kasar ta masa a matsayin zalunci.

Tsohon shugaban dai ya shafe shekaru a kurkuku tun bayan da sojin kasar suka masa juyin mulki, wanda a jiya kuma ya yanki jiki ya fadi a kotun da ake yi masa shari'a kuma rai yayi halin sa.

Kasashen duniya daban daban sun nuna alhini da takaicin su tare da yin ta'aziyya ga iyalan mamacin, hadi da nuna yatsan zargi ga gwamnatin da Shugaba Abdul fata Al-sisi take jagoranta.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top