AN kasa hakkokin maaurata zuwa kashi uku
na daya hakkin miji akan mata
na biyu hakkin mata akan miji
na uku hakkin tarayya tsakanin maaurata
Hakkin mata akan miji sune:

1.ciyarwa gwargwadon iko.
2.tufatarwa daidai iko.
3.shayarwa.
4.kayan kwalliya.
5.kayan tsafta.
6.gurin kwana.
7.kula da lafiya.
8.hakkin saduwa.
9.ilmantarwa.
10.girmamawa.
11.mutuntawa.
12.tausasawa.
13.yabawa ga abinci ko kwalliya ko tsafta.
14.nuna damuwa da ita.
15.sakar mata fuska da murmushi.
16.gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.
17.zama hira da tattaunawa da ita.
18.kiranta da suna mai dadi.
19.yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.
20.fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.
21.taimaka mata aikin gida ko dan kadan.
22.bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.
23.bata damar zabin tufafin da zata sauya.
24.mutunta iyayenta da danginta.
25.A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.
26.A  yaba mata idan tayi daidai.
27. kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.
28.banda duka.
29.banda zagi.
30.banda saurin fushi.
31.ka zama  miji mai tsafta.
32.ka zama miji mai kula da goge baki.
33.miji mai kwalliya.
34.miji bamai almubazzaranci ba.
35.miji bamai mai kwauro ba.
36.miji bamai shan taba ba.
37.miji bamai mai shan giya ba.
38.miji bamai yawon dare ba.
39.miji bamai  neman mata ba.
40  Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalansa.
41.miji mai yawan fada.
42.kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyali.
43.kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalansa suke ciki.
44.kada ka zama miji mai tsananin kishi.
45.kada ka zama miji mai yawan zagi.
46.ka nuna wa matarka cewa gamsu da yanayinta.
47.ka bata dama ta fadi raayinta.
48.kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.
49.ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.
50.yin wanka tare a wasu lokuta.
51.rera mata waka da kirari.
52.yin wasa da guje-guje.
53.kada ya zama miji mai zargi.
54.kada miji ya zama mai mugunta.
55.kada miji ya zama mai kushe.
56.kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.
57.kada miji ya zama mai ragwanci.
58.mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.
59.miji ya zama mai kaunar yayansa.
60.miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa
 Na biyu hakkin miji akan mata sune:

1.Ta rike masa amana, 
2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.
3. Ta kula da dukiyarsa
4. Ta  kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya
5. TA  girmama shi a gaban idansa
6. TA  kare girmansa a bayan idansa
7. Ta  so abinda yake so,  koda ba abin so bane a wajenta
8. Ta  ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta
9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.
10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi
11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi .
12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi
13.Idan ya bata kadan taga yawansa
14.Idan ya bata da yawa tayi godiya
15.Ta farka daga bacci kafin ya farka
16.Sai yayi bacci kafin tayi
17.Tayi hakuri idan yayi fushi
18 Tayi taushi idan yayi tsauri
19.Ta lallashe shi idan ya hasala
20.kada ta nuna raki a gabansa
21.kada tayi kuka alhali yana dariya
22.kada tayi dariya alhali yana kuka
23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu
24.kada ta matsa masa da bukatu
25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida
26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai
27.kada ta dinka kushe tsarinsa
28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta
29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta
30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau
31.Ta dinka boye abu mummuna
32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake shi ya warware ta
33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina
34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa
35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki
36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya
37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako
38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu
39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin da ya dawo
40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi
41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta
42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge
43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro
44.Tayi ado karshen iyawarta
45.Ta bayyana halaye masu kyau
46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai
47.Ta bayyana kanta a matsayin mace
48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai
49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta
50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so
51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna
52.Ta yafe masa idan ya munana mata
53.Ta karbi uzurinsa
54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa
55.kada ta dau azumi sai ya sani.
56.kada ta fita daga gida sai ya sani.
57.Ta iya girki kala-kala.
58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.
59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.
60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai
Na uku shine hakkokin tarayya tsakanin maaurata
1 Nunawa juna kauna da soyayya
2 Tarayya da juna cikin abinda ya sami dayan ko na farin ciki ko bakin ciki
3 kowa ya dinka yiwa abokin zaman sa kwalliya da tsafta.
4 kowa tsakanin maaurata ya zama mai kishin da uwansa
5 a sami amincewa juna
6 kowa ya bawa kowa daga cikin hakkin jin dadi da juna ta hanyar da shari'a ta amince.
7 kyakyawan zamantakewa tsakanin juna
8 hakuri da juna9 Amincewa juna
9 Farantawa juna rai.
10 su zama kamar abokan juna da yin shawara da juna
11 Nuna juna kauna daga bangaran kowa daga cikin su.
12 Girmama iyayan da yan uwan juna
13 Taimakon juna a lokacin da wani daga ciki ya gamu da jarrabawa.
14 Wani su dinka tona asirin juna a waje
15 Banda cin Amanar juna.
16 kada su dinka bayyana wani mu'amalar su ta auratayya.
17 Akwai gado a tsakanin su idan daya daga cikin su ya fara rasuwa.
Wannan sako ne ga dukkan maaurata su zauna suyi nazarin wannan sako kowa yaga abinda yake yi a ciki, domin mu gudu tare mu tsira tare
Allah ya bamu ikon kiyaye hakkin juna.
YA cika zukatan mu da kauna da soyayya da girmamawa tsakanin mu da iyalinmu.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top