Daga : Aliyu Muh'd Sani


Abin da masana suka fada shi ne; Kiristoci sun soki Annabi (saw) a kan auran mata tara (9), amma ba a samu sun soki aurensa da A'isha (ra) tana 'yar shekara tara (9) ba, har sai da aka samu wani Saurayin Dan Jarida mai bin Makarantar Mabiya hankali (Aqlaniy) a Misra, wanda ya yi rubutu a wata jarida mai suna "اليوم السابع" (Youm7), a ranar Alamis 16 Oct 2008, inda ya karyata Hadisin Bukhari da Muslim da sauran Malaman Hadisi da na Tarihi da suka tabbatar da cewa; Annabi (saw) ya auri A'isha (ra) tana 'yar shekara shida (6), ta tare tana 'yar shekara tara (9).
Shi wannan Dan Jarida dan kasar Masar ya yi karyan cewa; -wai- yana so ne ya kare matsayin Annabi (saw) don kar a soke shi da cewa; ya auri karamar yarinya, alhali kafin ya yi rubutun ba a san wani da ya yi suka a kan auren ba, sawa'un cikin Yahudawa da Nasara ko cikin Mulhidai.
Da ma wannan Dan Jarida ya shahara da sukar Hadisan Annabi (saw), musamman Sahihul Bukhari da Muslim, yana karyata Hadisan saboda sun saba ma hankulansu a matsayinsu na "Aqlaniyyun" masu fifita hankali a kan Alkur'ani da Sunna.
Asali ban so na tsawaita ba, kawai na so ne na ja hankalin Dr. Gumi a kan wata hujjarsa ta karyata Hadisin, inda ya yi da'awar cewa; wannan Hadisi Hisham bn Urwa ne ya ruwaito shi, shi kuma -a wajensa- mai rauni ne.
To da a ce Dr. Gumi ya shawarci masana Ilimin Hadisi, ya nemi bayani daga gare su da bai yi wannar magana da take nuna rashin saninsa ga Ilimin Hadisi ba, duk da yawan sukarsa ga Hadisan.
Don haka ya kamata Dr. Gumi ya san cewa; wannan Hadisi na shekarun auren A'isha (ra) ba Hisham bn Urwa ne kawai ya ruwaito shi daga Babansa Urwa ba, kuma ba Urwa bn Zubair ne kawai ya ruwaito daga A'isha (ra) ba, ga wasu kamar haka:
1- Imamu Zuhriy ya ruwaito shi daga Urwa:
عن الزهري، عن عروة، عن عائشة، «أن النبي صلى الله عليه وسلم تزوجها وهي بنت سبع سنين، وزفت إليه وهي بنت تسع سنين، ولعبها معها، ومات عنها وهي بنت ثمان عشرة»
صحيح مسلم (2/ 1039)
2- Al-Aswad bn Yazeed ya ruwaito shi daga A'isha (ra):
عن الأسود، عن عائشة، قالت: «تزوجها رسول الله صلى الله عليه وسلم وهي بنت ست، وبنى بها وهي بنت تسع، ومات عنها وهي بنت ثمان عشرة»
صحيح مسلم (2/ 1039)
A riwaya ta farko Imamu Zuhriy ya yi "Mutaba'a" ga Hisham bn Urwa.
A riwaya ta biyu kuma, Al-Aswad ya yi "Mutaba'a" ga Urwa din, ya jiyo Hadisin kai tsaye daga A'isha (ra).
To a nan kuma ban san abin da Dr. Gumi zai fadi a kan wadannan maruwaita guda biyu ba; Imamu Zuhriy, da Al-Aswad bn Yazeed Al-Nakha'iy?
A takaice, kafin kwararru a Hadisi su zo su ilmantar da mu a kan wannar mas'ala, ni dai na fadakar da mutane su san cewa; Magabacin Dr. Gumi a kan wannar mas'ala shi ne Dan Jarida dan Misra mai suna Islam Behairy, wanda ya shahara da sukar Sahihul Bukhari da Muslim, da sauran littatafan Hadisi, da rushe manyan tabbatattun mas'alolin Addini kamar Haddi na Shari'a da sauransu.
Allah ya shiryi Dr. Gumi.
A kasa ga hoton shi Dan Jaridan Islam Behairy



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top