( Daga Ahmed Abdullahi )
______£_____
Akwai kalaman da ya kamata kowace mace ta lakance su don furta su ga mijinta wanda rashin su kan iya harzuka Maigida a wani yanayi. Ga wadannan kalaman kamar haka:
> Yana da matukar muhimmanci mace ta shaidawa mijinta cewa " Ina matukar girmama ka saboda irin hidimar da ka ke yi muna a gida". Kowane magidanci yakan so Jin irin wadannan kalaman na jinjinawa kuma yana ba shi kwarin guiwar rubanyawa.
> Dole mace ta fahinci cewa babu abin da ya fi yarda muhimmanci a zamantakewa kuma miji yakan samu natsuwa da kuzari idan Uwargida ta nuna masa cikakken yarda don haka yake da muhimmanci musamman idan yana cikin yanayin kunci, ta zauna da shi ta ce masa " Na yarda da kai dari bisa dari"
> Kowane magidanci yakan so ya san ko yana yiwa iyalinsa jagoranci mai kyau, don haka akwai bukatar Uwargida ta nuna murna a kan kowane irin ci gaba mijinta ya samu a rayuwa saboda haka a irin wannan yanayi za ta iya furta cewa ' A gaskiya kana birge ni"
> Sai kuma kalmomin kauna wadanda akasarin mata ba su iya furta su ga mazajen su alhali kuma suna da matukar tasiri wajen gamsar da miji kan cewa ba wai sai yana da wani abin hannun sa ba ne, matarsa za ta nuna masa kauna don haka dole mace ta shaidawa mijinta cewa " Ina sonka"
> Dole Uwargida ta rika nuna kimar mijinta a gaban 'ya'yansu ta yadda yaran za su rika girmama shi.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment