Usman Mu’azu fitaccen furodusa ne a masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. A cikin tattaunawar da Aminiya ta yi da shi, ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga harkar fim. Ga yadda hirar ta kasance:

Ko me ya ja hankalinka har ka shiga harkar fim?

Tun ina makarantar sakandare nake kallon fina-finan Indiya da na Amurka, sai abin ya burge ni irin yadda suke amfani da fim wajen yada manufofin kasashensu da al’adarsu da dabi’unsu da sauran abubuwan da suka jibance su, don haka bayan samuwa da yaduwar fina-finan Hausa a shekarun 1990, sai na gano cewa idan har na shiga masana’antar fina-finan Hausa to zan iya ba da gudunmuwata wajen yadawa da kuma bunkasa al’adanmu da kuma addininmu. Mutum zai iya aika sako cikin sauki ta hanyar fim, sakon da zai dauki mai wa’azi tsawon lokaci bai yada shi ba.
Ko za mu iya cewa ka samu nasarar cimma burinka na sauya al’adun Hausa?
Ba wai muna sauya al’adun Hausa ba ne kamar yadda mutane da yawa suke ikirari, abin da muke kokarin yi shi ne mu fahimtar da Bahaushe asalin al’adarsa ta gaskiya da kuma addininsa na Musulunci. A takaice dai muna bayyana abubuwan da muka karanta a littattafan tarihi da magabatanmu suka rubuta ne, musamman ma ga wadanda ba su iya karatu da rubutu ba.

Ko wane kalubale ka fuskanta bayan ka fara harkar fim?
Babban abin da ke ci mini tuwo a kwarya shi ne mummunan kallo da mutane suke yi wa Kannywood, abin da yawancin lokuta suke mantawa shi ne a kowane fanni dole sai an samu mutanen kwarai da kuma bata-gari. Ko a gidajenmu ne akwai yaro mai da’a da kuma wanda ba ya ganin kan kowa da gashi. Kuma dukkansu mahaifansu daya. Masana’antar fim kamar kwalba take, duk abin da ka dura a ciki shi za ta zama, ko da ka zuba giya ko ruwa wannan kwalbar dai sunanta kwalba, abin da yake ciki ne zai bayyana yadda kwalbar take, jama’a suna yi mana kudin goro, suna shafa mana kashin kaji hakan ba adalci ba ne.
Kalubale na biyu shi ne, rashin isasshen jari don samar da ingantattun fina-finan da za su yi goyayya da sauran fina-finan duniya. A gaskiya muna bukatar kudi, idan har aka samu isassun kudi a masana’antar, za mu iya samar da kudin shiga ga gwamnati, kuma za mu bunkasa tattalin arzikin kasa tun da za mu samar da ayyukan yi ga ’yan kasa.

Wane sauyi ka ke ganin an samu daga lokacin da ka fara harkar fim zuwa yanzu?
Gaskiya an samu sauyi, tun daga bangaren jigon labarai zuwa kayayyakin aikin shirya fim. Mun samu ci gaba wajen na’urorin da muke daukar fim, ta wannan fanni za mu iya gogayya da fina-finan Hollywood na Amurka da kuma na Bollywood da ke Indiya, yanzu abin da muke bukata shi ne mutanenmu su samu horo don mu iya samar da fina-finai masu kyan hoto kamar na sauran kasashen da suka ci gaba.

Haka idan ka kalli fina-finan Kannywood a yanzu ba kamar da ba, za ka ga suna dauke da sakonni daya zuwa biyu, ko dai suna magana a kan al’ada ko kuma yada addinin Musulunci. Ina alfahari da kasancewa daya daga cikin wadanda suke yin hakan, zan kuma ci gaba da yin hakan don yada al’adunmu da kuma addininmu.
Ana tuhumar furodusoshi da ke Kannywood cewa ba su da aiki sai kwaikwaiyon fina-finan Indiya. Ko me za ka ce a kan hakan?
Haka yawancin masu kallonmu sukan yi irin wannan korafin, bayan mun samu wadannan korafe-korafen sai muka yanke hukuncin yin bincike. Binciken da muka gudanar mun gano cewa Bollywood ta shafe shekaru masu yawa, hakan ya ba su damar samar da fina-finai a kan kowace mas’ala da ta shafi dan Adam, wannan dalili ya sa ko da ma furodusa bai kwaikwayi wani fim din Indiya ba sai ka samu masu kallo sun ga kamanceceniya da wani fim din Indiya, amma a nawa bangaren ban taba kwaikwayon fim din Indiya ba, idan ma an ga wani fim dina ya yi kama da na Indiya to faduwa ce ta zo daidai da zama.

A kwanakin baya an ga ka mayar da hankali wajen shirya fina-finan barkwanci, inda ka shirya fina-finai irinsu ‘Karangiya’ da ‘Hedimasta’ da ‘Yaki Da Jahilci’ da sauransu, ko a yanzu za mu iya cewa ka sauya akala zuwa ga shirya fina-finan barkwanci ke nan?
A matsayinka na furodusa dole sai ka bugi jaki da kuma taiki. Wato ka rika shirya fim da ya shafi dukkan bangarorin dan Adam, a yanzu mutane sun fi bukatar labaran barkwanci don su samu sararawa daga halin da suka samu kansu a ciki na matsaloli, hakan ne ya sa muke shirya fina-finan barkwanci don mu bada gudunmuwarmu wajen nishadantar da masu kallo.
Ko zuwa yanzu ka shirya fina-finai kamar nawa?
Tun daga lokacin da na shiga Kannywood daga shekarar 2004 ke nan zuwa yau, zan iya cewa na shirya fina-finai kamar 113. 16 daga ciki a karkashin kamfanina mai suna Edpress Media Art Inbestment Limited.

Fina-finan da na shirya sun hada da ‘Ga Duhu Ga Haske’ da ‘Karangiya’ da ‘Sarauta’ da ‘Ga Fili Ga Mai Doki’ da ‘Maza da Mata’ da ‘Dan Marayan Zaki’ da ‘Hedimasta’ da ‘Garba Gurmi’ da ‘Yaki Da Jahilci’ da ‘Hangen Nesa’ da ‘Ummi Adnan’ da ‘Ashabul Kahfi’ da ‘Wuta da Aljanna’ da ‘Bashin Gaba’ da kuma na kwanan nan mai suna ‘Lantana’.
A cikin fina-finan da ka shirya wanne ya fi ba ka wahala?
Kowane fim yana da nasa kalubalen. Domin sai ka fitar da kowace rawa da ake so a taka a fim din yadda ya kamata. Amma dai fim din da ya fi ba ni wahala shi ne fim din ‘Dan Marayan Zaki’, saboda kasafin kudinsa, mun shafe wata shida kafin muka kammala daukar fim din, mun sha wahala wajen lura da jaruman fim din don kada su kara kiba ko su rame.

Ko kun samu riba bayan fim din ya shiga kasuwa?
Mun kashe akalla Naira miliyan 11 wajen shirya fim din, a lokacin da Naira miliyan hudu za ta shirya maka kayataccen fim. Amma Alhamdulillah, a makon farko da muka sake fim din a kasuwa muka mayar da kudinmu har muka samu riba. A lokacin kasuwancin fina-finai na garawa, mun samu riba sosai.
A ganinka ta yaya gwamnati za ta iya taimaka wa Kannywood?
Muna bukatar gwamnati ta shigo industiri don horar da ‘yan fim. A rika shirya wa ‘yan fim samina. A horar da jarumai da daraktoci da furodusoshi da sauran ma’aikatan shirya fim, musamman ma idan ka yi la’akari da kadan daga cikinmu ne suka samu horarwa a kan dabarun shirya fim.

Don haka idan gwamnati da sauran kamfanoni suka shirya horarwa, hakan zai taimaka mana mu yi gogayya da takwarorinmu da ke duniya. Idan ‘yan fim suka samu horo kamar yadda ya kamata, kuma suka rika shirya fina-finai masu inganci, to samun babban jari ba zai ba mu wahala ba. ‘Yan kasuwa za su zuba jari saboda za su samu tabbacin cewa kudinsu zai dawo. Mutanen da suke ci a karkashin Kannywood sun fi dubu 20, kama daga wadanda suke taimakawa a wajen daukar fim da ‘yan kasuwa da masu sinimomi da kuma masu tura fina-finai a waya da sauransu.

A kwanakin baya na je kasar Indiya, inda na yi kwas din wata shida kan dabarun shirya fim. Na fahimci ta hanyar fim za mu yaki munanan dabi’u da ayyuka da ake aikatawa a kasar nan.
Misali ta hanyar fim za mu iya magance matsalar shaye-shaye da tsaro da sauransu. Don haka idan gwamnati ta tuntube mu za mu iya shirya fim a kan wadannan matsalolin da na lissafa. A baya muna ilimantar da masu kallo illar wadansu cututtuka an kuma kawar da su. Don haka za mu iya shirya fina-finai a fannonin da gwamnati take so a fadakar a kai.

Satar fasaha wata matsala ce da ke ci wa Kannywood tuwo a kwarya, a ganinka ta yaya za a magance matsalar?
A yanzu yawancin mutane suna jin tsoron zuba kudinsu a harkar fim, ko da yake gwamnati tana iya bakin kokarinta a wannan bangare. A kwanakin baya ma na karanta a Jaridar Daily Trust labarin wadansu da aka tura gidan yari saboda satar fasaha, inda suke sayar da fina-finanmu ba bisa ka’ida ba, wannan abin a yaba ne. A namu bangaren ma muna da wani kwamiti da ke yaki da satar fasaha, kuma suna kokari sosai.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top