Kamar yadda aka sani kabeji na daga cikin ganyayyakin da ake ci musamman na marmari.
Akan kwada ganyen kabeji da kuli kokuma da main bature wato ‘Salad Crème’ ko kuma ‘Mayonnaise’ a ci haka nan ko kuma a hada da shinkafa dafaduka, danwake da sauransu.
Za kuma a iya dafa ganyen da shinkafa ko kuma a hada shi a faten tsaki da sauran su.
Duk da cewa cin marmari ake yi masa wannan ganye na Kabeji na da matukar amfani a jikin mutum.
Ganyen kabeji na dauke da sinadarin ‘Protein’ wanda ke gina jiki,’Vitamin C’ da ke warkar da ciwuka a jiki da sauran su.
Hanyoyi 9 da za a iya amfani da wannan ganye domin lafiyar jiki da maganin wasu manyan cututtuka
1. Kabeji na warkar da ciwon gabobin jiki da ciwon kafa (Arthritis).
Idan aka wanke ganyen kabeji sai a liliyashi ko da hannu ko kuma da kwalba ko dai wani abu mai santsi ya mike ta yadda za a iya nada shi ko a manna shi ganyen a jiki ko kuma inda yake wa mutum ciwo.
Bayan awa daya ko biyu sa za samu saukin ciwon da ake ji a jiki.
2. Yana kashe kwayoyin cuta da suke fadawa budadden rauni idan aka ji
Idan aka jajjaga ganyan kabeji sai a dibeshi a shafa a shiwon. Yin hakan na taimakawa wajen kashe kwayoyin cututtuka da ka iya shiga ciwon musamma wadanda ke sa ciwo ya zama gyambo.
3. Yana warkar da ciwon nono da tsayar da ruwan nono idan an gama shayarwa
Ga matan dake shayarwa ko kuma suka yaye ‘ya’yan su ganyen kabeji na hana ciwon nono ya kuma hana zuban ruwan nonon bayan yaye.
Mace za ta dauki ganyen ta lullube nononta da shi da daddare sannan ta cire ganyen washe gari.
4. Cin kabeji na rage kiba a jiki
Duk iya cin da mutum zai yi wa kabeji ba zai kara kiba ba illa ma ya rage saboda kabeji na dauke da sinadarorin dake rage kiba a jiki.
5. Yana warkar da cutar gyambon ciki wato ‘Ulcer’.
Mai dauke da gyambon ciki ‘Ulcer’ zai samu sauki idan ya juri cin ganyan kabeji danye wanda aka kwada da kuli ko kuma da man bature ko kuma dafaffe a cikin shinkafa ko fate ko kuma ya sharuwan ganyen kabejin.
6. Yana kawar da ciwon kai.
Kafin a kwanta da daddare sai a tsinki ganyen kabeji a lullube kai da shi. Yin haka zai hana ciwon kan da ake ji.
7. Kabeji na kawar da laulayin haila
Mai laulayin haila za ta samu sauki ida ta juri cin ganyan kabeji sannan tana dora ganyen a maranta kafin ta kwanta barci.
8. Kabeji na hana saurin tsufa.
Kabeji na hana sauri tsufa idan ana wanke fuska da ruwan kabeji kokuma idan aka juri cin sa.
9. Yana kuma kara tsawon gashi a kai.
Kabeji na dauke da sinadarin ‘ Vitamin E da silicon wanda ke hana gashin mutum tsinkewa sannan ya kara tsawon gashin.

® Premiumtimes


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top