Gwamnatin kasar Brazil ta kwace wasu manyan kadarorin dan wasan kwallon kafa na kungiyar PSG

- Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne bayan ta same shi da laifin kin biyan haraji na tsawon lokaci mai yawa

- Gwamnatin ta bayyana cewa a yanzu haka tana bin dan wasan bashin haraji kimanin fam miliyan 14

Matsalolin da dan wasan kwallon kafa na kungiyar PSG, wato Neymar ke fuskanta ya karu, bayan hukumar karbar haraji ta kasarsa Brazil ta kwace wasu manyan gine-ginensa da kuma wasu kadarorin sa da ya mallaka, bayan ta sameshi da laifin cinye lokaci mai tsawon gaske ba tare da ya biya harajin da kasar ke binsa ba.

Hukumar karbar harajin ta kasar Brazil ta sanar da cewa yawan harajin da take bin Neymar ya kai kimanin fam miliyan goma sha hudu, hakanne ya tilasta mata kwace kadarorin nasa kimanin guda 40.

Amma hukumar ta ce kwace kadarorin da tayi ba yana nufin ba zai iya amfani da su bane, yana da ikon yin amfani da su, amma kwacewar na nufin an haramta mishi sayar da su ko kuma ya sanya wasu mutane a huldar kasuwanci da su.


Jami'an hukumar karbar harajin sun sanar da cewa tarin harajin da ake bin dan wasan tun na shekarar 2013 ne, lokacin da ya sauya sheka daga kungiyar Santos ta kasar Brazil zuwa kungiyar Barcelona.

Matsalar kin biyan harajin dai ya zama kari akan manyan matsalolin da dan wasan ke fuskanta a 'yan kwanakin nan, inda suka hada da zargin shi da ake yi da yin fyade da wata mata ke yi masa, amma dai dan wasan ya fito ya musanta ikirarin matar na fyaden.

Bayan haka kuma an yiwa dan wasan wani gargadi mai ban tsoro wanda shugaban kungiyarsu na PSG ya nuna cewa ya gama shiri tsaf domin sayar dashi, idan har ya cigaba da nuna musu rashin da'a a kungiyar tasu.

Idan ba a mance ba kwanakin baya dan wasan yayi amfani da hannunsa ya daki wani dan kallon kwallo a lokacin da suka tashi daga buga wasa.

A kwanakin baya jaridar Forbes ta kasa Amurka ta ruwaito cewa dan wasan shine na uku a cikin 'yan wasan da suka fi kowa daukar kudi a duniya, na daya shine dan wasan Barcelona, wato Lionel Messi, sannan sai Christiano Ronaldo, wanda yake a kungiyar Juventus.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top