Fitattacen malamin addinin islaman nan  Shiekh Abdallah Gadon Ƙaya ya ce abubuwan da su ke faruwa na kashe-kashe da akeyi a jihar Zamfara yafi ƙarfin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Da yake bayani a wani faifan bidiyo daya wallafa  a shafinshi na Facebook , Sheikh Abdallah ya bayyana abubuwa na rashin dadi da suke faruwa yanzu a Najeriya bisa son zuciya da neman duniya na wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa da kuma jagororin Arewa suke dashi.

“Akwai wadansu daga cikin manyan kasar nan, lokacin fadar sunansu bai yi ba amma na sansu, manya ne kuma ‘yan arewa ne. Akwi arzikin ma’adanai a Zamfara, don haka, su suke da hannu

Sheikh Gadon Kaya yayi kausasan kalamai inda har ta kai shi ya bayyana dalilan daya sa aka fara tada fitina a jihar Zamfara.

Bayanan da yayi sunyi nuna da kiran cewa babban dalilin tada fitina a jihar shine domin a dibi ma’adanai na jihar, har ma ya kafa misali da dajin Sambisa inda yace a saboda danyen mai da yake daji yasa aka fara fitintinu a domin a kautar da hankalin gwamnati waje sace albarka tun kasa.

Daga bangare guda kuma yace shugaba Muhammadu Buhari yana da masaniya akan duk abubuwan da suke faruwa a Zamfara, sai dai yace shugaba bashi da wani karfin da zai iya yin abu saboda al’amarin yafi karfinshi.

“Shi shugaban Kasa (Buhari) da kuke gani, wallahi yasan wannan abin, amma wallahi yafi karfinshi, sai dai da taimakon wadansu.

“Idan ya tura Sojoji ko ‘Yan Sanda, suma suna da masu basu umarni. Cikin manyan Sojoji suma suna da son su sami kudi.”

Sai dai al’umma da dama na ganin cewa shugaba Buhari ne yake da damar da zai yi duk mai yiwuwa wajen daƙile waɗanann abubuwa marasa daɗi kama daga garkuwa da mutane, harbin kan mai uwa da wabi da saurarn al’amura da suka kasance suna neman gagarar kundila.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top