Daga Taskar Ummancy

Sirrin soyayyan aure da dattijon namiji shine mace ta san cewa zata yi kishi da matan da suka girmemata ne, wata kila kuma sun ma haifeta, irin wadannan mazan suna bukatar ganin mace da zasu aura tana mutunta matansa na gida musamman uwargidan kamin ta shiga da kuma bayan ta shiga. Haka kuma duk da irin kaskantar da kansa da zai yi a gabanki ganin yana nemanki da aure kuma gashi zai iya kasancewa sa'an mahaifinki, yana da kyau ki mutuntashi kuma ki dauke shi da daraja ba wai kuma ki maidashi wani boyi-boyi ba saboda zai rufa miki asiri ya aureki a matsayinsa na tsoho. Hakan zai baki martaba da daraja wajen 'ya'yansa da kuma abokansa dama wasu masu sanya idanuwa game da soyayyan naku.

Irin wadannan mazan basu cika kawo sako da kansu ba, akasari suka samu wani da suka aminta da shi kokuma wani babba daga cikin yaran gidansu su rika aika ne wajen matan da suke so da aure. Anan sirrin maza irin wadannan dattijan shine ki tabbatar 'yan aikensu kina mutuntasu, haka kuma kada kiyi wani abu, ko ki fadi wata kalma ko aikata wata dabi'a da zai iya kawo shakku a idanuwan dan aiken ko cusa masa wani kokwanto a zuciya yadda zai yi tunanin cewa maigidansa, ko mahifinsa ko kakansa zai auro mace ballagaza.

Wanni sirrin irin wadannan mazan shine, suna da matukar yiwa macen da suke nema da aure hidima, hidimar da wani lokacin yana wuce hankali, koda suna da shi ko basu da shi, abunda irin wadannan mazan basu so shine suyi maki kyauta kike karba. Suna bukatar ganin duk wani kyautar da suka yiwa macen da suke nemanta da aure ta sa hannu biyu ta karba tare da da nuna farincikinta da annashuwa. Sai dai kuma kada hakan ya baki damar yawan yi masa aike da bani-bani, ko kuma yawan gabatar masa da bukatunki dana kawaye ko iyayenki a duk lokacin daya zo wajenki. Duk da yake idan mai haline ba zai taba nuna miki gajiyawa ba ko kuma fushinsa a zahiri ba, sai dai kuma hakan yana iya zubar miki da mutunci a wajen na kusa da shi, shi kuma zai dauka cewa iyayenki ba dattawa bane, haka kuma irin wadannan mazan babu wanda yakaisu gori, kada kiyi mamakin idan watarana ya cemiki shi yake ciyar da gidanku.

Da yake sun manyanta kuma sun saba da karabniya da 'ya'ya da jikoki, kuma dadewarsu a duniya yasa suka fahimce halaye na mata dai dai gwargwado, mazan da suka manyanta masu neman aure maza ne da suke sha'awan ganin macen da zasu aura kullum a cikin kwalliya, haka kuma suna son mace mai yawan shagwaba tabkar karamar yarinya ko kuma jika a gaban kakanta. Wani abun sha'awa da irin wadannan mazan shine yana da wuyar gaske su nemi macen da zasu aura da lalata koda kuwa suna da matsaniyar tsohuwar karuwace.

Kamar yadda kika yi hakuri a lokacin soyayyar neman aurenki da namijin daya manyanta haka zaki ci gaba da hakurin bayan kunyi auren. Munyi bayani a baya irin matsalolin dake tattarae da soyayya da namijin daya manyanta, hakama zaman aure dashi yake da nasa matsalolin.

Akasarin dattijawan maza dai yana da matukar wahala a rasasu da mace a lokacin da suke neman wani auren, haka kuma ana iya samunsu da 'ya'ya manya wasu lokutanma har da jikoki. Don haka duk macen data zabawa kanta zaman aure da irin wadannan mazan dole ne sai ta hada da gagarumin hakuri ko tana gida daya da sauran matansa ko kuma kowacce da muhallinta.

Mafi yawan irin wadannan mazan da suka manyanta kuma suke bukatar aure, ba rashin jin dadin zama da tsoffin matansu bane basa yi, sai dai wasu loluta kamar yadda bincike ya tabbatar matan nasu na iya tsofar da bazasu iya gamsar dasu ba a lokutan jima'i. Haka kuma wasu tsofin magidanta giyar kudi ne ke dibarsu suji ko ba komai ai gara su samo wata mace mai dan galmi-galmi su aura domin su burge abokansu. Wasu lokutan kuma abokai ne a tsakankaninsu suke yiwa tayi 'ya'yansu ga junansu.

Koma dai da wace hujja ko dalili mace ta yanke shawarar auren namiji daya manyanta, babban sirrin zama da shi shine ta tabbatar da cewa bat nunawa matansa, 'ya'yansa, jikokinsa, 'yan uwansa da abokansa gadara da iyayin da zata iya fiskantar matsala dasu ba. Kamar yadda muka yi bayani a baya, a lokacin da dattijon na miji ya yanke shawarar auren mace, bai cika canza ra'ayi ba koda kuwa ya fahimci wani illa da macen da yake sonta da auren ba, haka kuma lokacin daya aure mace bai cika barin wani matsala a tsakaninsu yana bata masa rai ba ganin cewa yana da kwarewar zama da mata da kuma sanin irin matsalolin mata da hanyar warwaresu ganin shima ana kawo irin wannan gabansa na 'ya'yansa ko jikokinsa yana magacesu.
Sai dai babban matsalar da macen data aure dattijon namiji zata iya fiskanta a zaman aurenta da mijin nata shine idan har ta sake wata matsala ya shiga tsakaninta da matan wannan mijin nata, ko kuma 'ya'yansa. Wanda irin gallazamata na karkashin kasa dana zahiri yana iya sanyawa ta gudu ta bar ladanta. Babban sirrin zama da irin wadannan magidanta shine ki tabbatar da cewa babu raini a tsakaninki da matansa duk da yake yanzu abunda suke ji wajen dattijon kema kina danawa, haka kuma a wannan lokacin idan matansa marasa fahimta ne da tsoron Allah zaki ga abubuwa da dama da cusa bakin ciki da takaici tumma ba ace kuna gida daya ba ganin su sun tasanma tsofa kekuma yanzu kike more mijin nasu dasu ci kurunciyan aure tare amma gashi yanzu sun zama 'yan kallo.

Dole ki dauka cewa wannan matan da yanzu kike zaman kishiyoyi tare tamkar iyayen kine su, don haka duk wata bakar magana ko habaicin da zasu yada miki ki kauda kunnenki tamkar baki ji ba. Haka kuma kiyi kokakrin jawo wasu daga cikin 'ya'yansu ko kikokinsu da kika fahimci cewa masu saukin kaine da fahimta kusa dake domin kokarin nuna masu halin da kike ciki cikin hikima da dabara. Haka kuma ki tabbatar da cewa kin samu natsuwa sosai a duk lokacin da kika ga wani abu ba dai-dai ba a gidanki ganin zama da tsaffin mata a matsayin kishiyoyi, zama ne da mace take bukatr darasi a kansa ganin irin kissan da kisisina na gadar zare da irin wadannan matan zasu iya shirya mace ta fada idan bata yi hankali ba.

Haka kuma wani sirrin da zaki iya dauke hankalin tsohon mijin nan naki dashi shine iya kwalliya da kuma tsaftace jiki da muhalli. Shi na miji ko kazami ne yana sha'awar ganin cewa yana zaune da mace mai tsaffta. Haka kuma irin wadannan mazan ko kura bai kaisu kwadayin nama ba idan masu lafiyan hakora ne, idan kuma ba masu shi bane kada a raba ki da shirya masa 'yar wata ferfesu na kaza ko na kifi a duk lokacin da zai shigo gidanki ko dakinki.

Maza masu yawan shekaru sune mazan dasu kafi sha'awar ganin mace da manyan nonuwa ko kuma tsayayyun nonuwa, bincike ya tabbatar da cewa akasarin manyan maza masu shekaru da suke sha'awar kara aure babu abunda ke sasu hakan irin sha'awar ganin suna wasa da mikankun nonuwan budurwa ko karamar bazawara idan suka ga cewa matansu na gida sun tsufa.

Don haka a duk lokacin da zaki yi kwalliyarki na jiran miji, ki tabbatar da cewa kin yi shigar da zasu fito da hantsarki sosai domin kwantar da hankalin dattijon mijinki. Haka kuma iya tafiyarki shi kansa wani sirri ne na zama da dattijon na miji, domin a lokacin daya kyalla idanuwa yaga cewa kina tafiya jikinki na kadawa nan take keji tsohuwar tsuminsa yana tashi.

Haka kuma a duk lokacin daya shigo da abokansa wadanda suma watakila masu shekaru ne, to ki tabbatar da cewa kin karbesu hannu biyu-biyu, kuma ki nunawa mijin naki so a gaban wadannan abokan nasa har sai sun gamsu da cewa tabbas abokinsu yana cikin wani sabon rayuwa na zamantakewan aure, wanda hakan zai sasu suma suyi sha'awar idan suna da halin yi.

Bafa ina nufin cewa ki kwanta a kansa ko ki sumbace shi a gabansu bafa, a'a, abun nufi shine ko ta hanyar hira ki tabbatar masu da cewa wannan mijin naki yafi saurayi dan shekaru 17 a wajenki. Da kuma nuna masu cewa baki bukatar jimawansa a waje da makamantar irin wadannan wasanni na baki wanda wasi sako ne da mai hankali yana iya fahimtar abunda ke dauke cikinsa.

Sirrin zama da magidantan da suka tsofa shine, a kullum ki dauke shi tamkar kina auren saurayi ne, kada ki kyamace shi ganin akasarin manyan magidanta ana iya samunsu da wasu halaye irin na tsofa. Haka kuma ki tabbatar da cewa yadda zaki yi soyayyar zaman aure da na miji mai karancin shekaru haka shima zaki yi da shi. Haka kuma ki cire a ranki cewa kina zaman aure ne da dattijon daya yayi sa'ar mahaifinki, saki jiki ki wahala kiyi soyayayyar zaman aurenki da mijin naki.

Sai dai kuma manyan matsalolin da mata suka fi fiskanta a lokacin zaman aure irin wannan shi ne na rashin samun haihuwa a wasu lokutan da kuma ishenshen kwaciya ta jima'i ga macen data ke da bukata da yawa.

ummanncyumar@gmail.com


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top