Marigayin, Luka Yusuf, wanda ya kasance Kirista ne kuma mafarauci a kauyen Kubo-Kanakuru a karamar hukumar Shani da ke jihar Adamawa, ya gayyaci abokansa Musulmai guda 7 domin raka shi kauyen Borong inda zai gana da iyayen amaryarsa domin kammala shirin daura musu aure.
Kauyen Kubo-Kanakuru, da ke kusa da iyakar jihohin Borno da Adamawa, ya kasance gari da Kirista da Musulmi ke zaune lafiya duk da kasancewa mafi yawan al'ummar garin Musulmai ne.
Kasancewar ango Yusuf da abokansa duk mafarauta ne, sai suka yi shiga irin ta 'yan farauta tare da daukan bindigun baushe da kuma kayan goro da zasu kai wa iyayen amarya. Sun yi sallama da gida kafin tafiyarsu, tafiyar da suke saka ran zuwa su dawo lafiya.
Kafin su hau hanya, Yusuf ya sanar da wani mutum da ke can kauyen Borong domin ya sanar da jama'a cewa za su zo don kar ganinsu ko jin laarin isowarsu ya firgita mazauna kauyen.
Amma bayan Yusuf da tawagar abokansa sun hadu da mutumin da aka bawa sakon sanar da jama'ar kauyen Borong zuwansu, wanda shine kuma zai musu jagora su karasa zuwa kauyen Dilli; inda amaryar da iyayenta ke zaune, sai wasu mazauna kauyen da su ka hango su daga nesa a kan babura suka garzaya suka fada wa jama'a cewa ga makiyaya nan sun taho su kawo hari garin.
Mutanen kauyen sun gaggauta sanar da jami'an 'yan sanda halin da ake ciki, wanda ba tare da bata lokaci ba suka iso wurin tare da tafiya da ango Yusuf da abokansa zuwa ofishinsu domin tabbatar da cewa jama'a basu far musu ba bisa rashin sani.
Sai dai hakan bai tserar da su ba, domin ba a dade da kai su ofishin 'yan sandan ba sai ga dandazon jama'ar gari sun cika bakin ofishin 'yan sandan tare da gudanar da zangar neman a barsu su hallaka Yusuf da abokansa bisa tunanin cewa makiyaye ne.
Duk bayanin jami'an tsaro domin ganin jama'ar sun fahimci cewa Yusuf da abokansa ba makiyaya bane ya ci tura, wanda daga bisani ma suka bijire wa duk wani yunuri na tarwatsa su tare da yin amfani da karfin tuwo wajen kusta kai cikin ofishin 'yan sandan tare da hallaka Yusuf da abokansa.
Mutanen garin sun wulla gawar Yusuf da abokansa a wani tafki.
Alhassan Danladi, mutum guda tilo da ya tsira, ne ya sanar da jaridar Daily Trust yadda lamarin ya faru.
Danladi ya tsira ne sakamakon faci da tayar babur dinsa ya yi, lamarin da ya saka ango Yusuf da ragowar abokan tafiyarsa suka tafi suka barshi a baya.
Ya kara da cewa sai bayan an wulla gawar abokansa a ruwan ne sannan wasu suka bayyana cewa sun gane fuskar marigayi Yusuf.
®Legit
©HausaLoaded
Post a Comment