Hukumar dabbaka koyarwan addinin Musulunci Hizbah ta damke wasu samari hudi a jihar Kano kan zargin daura auren wasa a shafin ra'ayi da sada zumunta na Facebook.
Hukumar Hizbah ta bayyana a ranar Laraba cewa wannan abu da matasan suka aikata isgilanci ne ga addinin Musulunci kuma hakan babban zunubi ne.
Kwamandan Hizbah a jihar Kano, Abba Sufi, ya bayyanawa AFP cewa: "Mun damke mazajen hudu da suka shirya auren Faceboon wanda ya tayar da kura cikin al'umma."
"Mun damkesu ne kan laifin isgilanci ga abu mai muhimmanci irin aure."
An damke wadannan matasa ne ranar Talata, bayan labari ya yadu a fadin Najeriya musamman arewa kan yadda aka daurawa wasu matasa biyu aure tare shaidu a Facebook.
Angon, Sanusi Abdullahi, ya bayyana cewa wasa yakeyi lokacin da ya biya kudin sadaki dubu ashirin domin auren wata budurwa wata yar garin Maiduguri kuma cewa zata tare a gidansa.
An kamashi tare da abokansa uku wadanda suka tsaya matsayin shaidu da wakilai a daurin auren.
Wannan abu ya tayar da kura a Arewacin Najeriya musamman malaman addini inda suka yi kira ga hukumar ta hukunta wadannan matasa.
Kwamandan Hizbah ya ce abin ya kai ga mutane sun fara yiwa Angon barazanar kisa kuma wani ya kai masa hari yayinda ya fito daga Sallar Magariba ranar Litinin.
©HausaLoaded
Post a Comment