Wata babbar kungiya dake fafutukar wanzar da zaman lafiya a Kaduna ta karrama Dr Ahmad Gumi

- Kungiyar ta bayyana cewa sun zabi Ahmad Gumi ne saboda jajircewar shi da kuma fadar gaskiyarsa ba tare da tsoro ba

- Kungiyar ta kara da cewa Sheikh Ahmad Gumi shine Malami guda daya tilo da baya jin tsoron fitowa baro-baro ya fadawa shugabanni gaskiya a Najeriya

Wata kungiya mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya da taimakon marayu a Kaduna mai suna "Manufa Charity Foundation" ta karrama sanannen malamin nan mazaunin Kaduna da lambar girma wato Dr Ahmad Gumi, sakamakon jajircewar shi wajen fadin gaskiya komai dacin ta ba tare da fargaba ba.

Da yake mika mishi lambar girmamawar a gidan Malamin da ke Kaduna, Shugaban Ƙungiyar Ibrahim Manufa ya ce babban dalilin da ya sa suka zabi Dr Gumi domin karrama shi ya biyo bayan kwazon malamin ne wajen fadakar da jama'a da wayar musu da kai wajen sanin halin da kasa ke ciki ba tare da nuna wata fargaba ba.



Manufa ya kara da cewar, samuwar Malami irin Dr Gumi cikin al'umma rahama ne, saboda shi Malami ne wanda ya fita daban da sauran malamai, ya nesanta kansa daga neman tara abin duniya ko nuna fadanci ga wani, wannan ya sanya ya zama malami guda daya tilo a Najeriya da ke gayawa shugabanni gaskiya ba tare da tsoro ba.

A jawabin godiya da ya yi, Dr Gumi ya jinjinawa Ƙungiyar Manufa Charity Foundation bisa ga kokarin da ta ke yi wajen taimakon jama'a musamman marasa galihu, sannan ya yi addu'ar sauran jama'a za suyi koyi da tsare-tsaren kungiyar na taimakon al'umma domin samun nasara.

® Legit

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top