An bayyana kisan maza da mata ke yi a Kano da cewar ba sabon abu bane, wata al'ada ce wacce ta dade a tsakanin Mata a Kano.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani Dattijo mazaunin garin Kaduna mai suna Alhaji Isiyaku Ahmad Kauran Wali, a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Kaduna.

Kauran Wali ya kara da cewar, ga duk wanda ya san tarihin Matan Kano, ya san da cewa sun dade suna hallaka Mazan su, musamman Masu kudin Kanawa ta hanyar zuba guba cikin abincin su, domin su sha su mutu, su kuma su gaji dukiya.

Dattijon ya cigaba da cewar wannan ya sanya a tarihin masu kudin Kano a shekarun baya basa cin abincin gidan su, sai dai suje waje su sayi abinci su ci domin kaucewa cin guba.
"Sai dai a yanzu abin ne ya canza sabon salo, maimakon amfani da guba sai suka koma amfani da wuka wajen yin kisan" inji shi.

Kauran Wali yace yana ganin hakan bai rasa nasaba a yanzu na yawaitar kallace kallacen fina finai da suka yi yawa musamman a kasar Kano, inda ake shigo da sabbin wasu al'adu wadanda suka yi hannun riga da rayuwar Malam Bahaushe.

Dangane da alakanta kashe kashen da wasu ke yi da maganar mai Martaba Sarkin Kano kuwa, Isiyaku Kauran Wali ya ce ko kadan maganar ba haka take ba, da kyakkyawar manufa Sarki yayi maganar, rashin fahimta ce ta sanya ake zargin shi, ko kuma wata manufa da ake da ita ta wani abu daban.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top