Daga Khadija Garba Sanusi

 A yammacin yau ne Laraba 10/7/2019 Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kammala samarwa wasu daga Cikin Dalibai 370 yayan talakawa Gurbin karatu a Jami'ar MEWER UNIVERSITY dake Kasar India akan fannonin Daban-daban na ilimi Wanda Gidauniyar sa ta KWANKWASIYYA DEVELOPMENT FOUNDATION zata dauki nauyinsu zuwa kasashe daban-daban na Duniya.

 zuwa yanzu dai Kwankwaso ya ziyarci Jami'o'i guda biyu akasar ta India a Cigaba da zagayen nemawa Daliban gurbin karatu da yakeyi akasashen Duniya a kakar karatu ta bana Wato (2019/2020 Academic Session).

 Sanata Kwankwaso Yana tare da Rakiyar Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Kebbi Eng. Abubakar Sadiq Argungu.





Kwankwasiyya Reporters Nigeria

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top