Lamarin ya haddasa tashin hankali a cikin harabar majalisar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa anyi gaggawan daukar daya daga cikin jami’an yan sandan zuwa asibitin majalisar dokokin da miusalin karfe 1:55 na rana.
Idon shaida da dama da ke wajen, sun bayyana cewa lamarin ya afku ne a lokacin da masu zanga-zangar suka yi kokarin kutsa kai cikin majalisar ta karfin tuwo.
“Sun harbi jami’an yan sanda uku. Daya daga cikinsu ma kamar ya mutu,” inji wani idon shaida.
An kuma tattaro cewa yan Shi’an sun cinna wa wasu motoci da aka ajiye kusa da mashigin majalisar wuta yayinda aka karo jami’an tsaro zuwa wajen da lamarin ke faruwa.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, jami’an yan sanda sun rufe mashigin majalisar dokokin yayinda karan harbi a sama ya karade ko ina.
Kamar koda yaushe yan Shi'an na zanga-zanga ne akan ci gaba da tsare shugabansu, Ibrahim El-zakzaky wanda ke kulle tun a 2015.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Al’umman babbar birnin tarayya sun bayyana ayyukan kungiyar yan Shi’a a Abuja a matsayin abun damuwa kuma hakan na iya zama barazana ga kwanciyar hankali da tsaron yankin.
Sun bukaci hukumomin tsaro da su gargadi kungiyar, su kuma tabbatar da tsaron mutanen birnin.
©HausaLoaded
Post a Comment