....Magana Ta Fito

Yanzu haka Hukumar EFCC Ta karbi takardun koke gurfanar da Tsohon Gwamna jahar Zamfara Yari akan yanda shida abokansa suka kwashe dunkiyar Alummar jahar Zamfara ya banza. Dr. Sani Abdullahi Shinkafi Ya rubuta takardar Zargin

1- Naira Biliyan ashirin da biyar (25,000,000,000:00) Da aka baiwa wani kamfani Mallakar Abba Aleiro da sunan sanya wuta a kananan hukumomi 14. Ba tare da an bi hanyar da ta dace wajen bayar da kwangilar ba, Wanda haka ya sabawa tanadin dokar bayar da kwangila ta Shekara 2007. Haka zalika kamfanin ba shi da karfi da MA kwarewar yin aikin da kamfanin ya ke Da ita. Kari akan hakan har yanzu kamfanin bai Kammala Kashi 30 cikin 100 na aikin ba. Kuma an yi amfani da kayan da aiki Marar inganci wajen aikin.

Dan haka ya yi kira ga hukumar da ta shigo cikin wannan barahira ta hanyar bincikar yadda aka biya kamfanin naira Biliyan ashirin (N20,000,000,000; 00) a asusun Gwamnatin jahar Zamfara duk da ba a Kammala aikin ba..

2. Zargi- EFCC  ta binciki Abdulaziz Yari akan yadda ya yi ta amfani da dukiyar jahar Zamfara yana daukar shatar jirgin kasaita a duk mako naira miliyan goma ( N10,000,000,000) makonni 56 a hadi da Shekaru 8 akan kudi naira Biliyan hudu da miliyan dari hudu Da tamanin (N4.480,000,000,000 ) baya ga tafiye-tafiye da ya yi ta yi a kasashen Saudi Arabia, Dubai, China, Europe da America da sauransu. Wanda in aka hada Hancin kudin za su Kai Biliyan uku. Amma a Shekaru takwas ba tare da ya gayyato ko da masu sanya hannun jari daya daga kasashen ketaren zuwa jahar Zamfara ba.

3. Zargi -EFCC tabinciki yadda tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar kai kwai ga daliban sikandire har naira miliyan arba'in (N40,000,000:00) duk wata ga kamfanin Rufai Farms Mallakar tsohon gwamnan jahar Zamfara Sanata Ahmed Sani (Yariman Bakura ). Duk Wata miliyan arba'in. (N 40 Million) in hada Watanni sha biyu sau takwas kudin sun kama naira Biliyan uku da miliyan dari takwas Da arba'in (N3.840,000,000:00). Wanda aka baiwa tsohon gwamnan Kai tsaye a fitar duk Wata zuwa ga kamfanin har a cikin watannin Hutu. dan haka hukumar ta bincike akai.

4 Zargi -shine yadda gwamnan ya bayar da kwangilar gina tituna a kananan hukumomi 14 akan naira Biliyan saba'in da biyar ba tare da biyar dokokin bayar da kwangilar ta 2007 ga kamfanin da ya yi kwangilar ba. Haka zalika, zuwa yanzu wasu ayukkan har yanzu ba su Kammala ba, Amma an biya sama da Kashi 80 cikin dari na kudin ga kamfanonin Da su ka yi aiki.

5. zargi- EFCC  ta binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta kashe naira naira Biliyan biyu da sunan Zaben kananan hukumomi a cikin kwanaki goma na karshen mulkin Gwamnatinsa Wanda kowa yasan bawai zabe akayiba face lakata dukiyar al'umma da sunan zaben karya.

Daga Basheer Muhammad Bmg Gusau


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top