Daga Datti Assalafiy

Gwamnatin Nigeria tana zargin shugaban kungiyar shi'ah (IMN) Malam Ibrahim Yakubu Al-zakzaky da laifin cin amanar Kasa ta hanyar kokarinsa na kirkiran kasa a cikin kasa, da laifin rashin biyayya da da'a wa dokokin gwamnatin Nigeria, har abinda ya faru a Gyallesu Zaria ya faru!

Matakin farko da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi amfani dashi na ajiye shugaban kungiyar shi'ar a gidan kurkuku yayi daidai, kuma sojojin sun kyauta da ba su kashe shi ba a wannan lokacin, amma lokacin da kotu tace a sakeshi to lallai kuwa da shugaba Buhari yayi hakuri ya sake shi ta hanyar bin umarnin kotu.

Akwai hanyoyin da gwamnatin shugaba Buhari za ta bi ta mayar da shugaban shi'ah Yakubu Ibrahim Zakzaky a matsayin marar amfani a cikin al'umma bayan tabi umarnin kotu an sakeshi, gwamnati zata iya masa daurin talala a cikin 'yanci, Misali kullun ace dole sai ya kai kanshi gaban DPO na yankin garinsa (Zaria), sannan a hanashi Visa na fita Kasar waje.

Bayan haka, gwamnati tana da iko ta rufe dukkan account dinshi, sannan a toshe duk wata hanyar da yake samun kudaden shiga sai wanda zai biya bukatun kanshi da na iyalanshi, tunda ba 'dan kasuwa bane, kuma ba ma'aikacin gwamnati bane, sannan gwamnatin Nigeria ta saka ido sosai akan dangantar diplomasiyya tsakaninta da Kasar Iran musamman akan irin taimakon da Iran take baiwa kungiyar Zakzaky.

Yana daga cikin ajandar kungiyoyin leken asiri da tattara bayanan sirrin tsaron duniya na manyan kasashen Yahudu da Nasara irin su MOSSAD-Isra'ila, CIA-Amurka, DGSE-Faransa, BND-Jamus, SIS/M16-Ingila da sauransu, shine ya zamto tsaron Nigeria yana karkashin kulawarsu, suna ganin idan sun juya tsaron Nigeria kamar sun mallaki tsaron nahiyar afirka ne, da kuma tattalin arzikin nahiyar, tunda da ma su sukayi mulkin mallaka suka sace arziki.

Wadannan kungiyoyin leken asiri na kasashen turawa suna da wakilansu a nan Kasarmu Nigeria, wakilansu ne sukayi amfani da shugaban Boko Haram na farko Muhammad Yusuf domin a rusa arewa, sune sukayi tsayuwar daka sukayi belin Muhammad Yusuf saboda wannan manufar, idan fadan yafi karfin gwamnatin Nigeria sai dakarun turawa da na yahudawa su shigo aikin kwantar da tarzoma, su lalata tarbiyyan al'ummar arewa, sannan su sace mana arziki ta karkashin kasa, gashi dai har zuwa yanzu ba su ci nasara akan wannan ba.

Su ne suka karfafi shugaban tsageru na kungiyar masu rajin kafa Kasar Biafra (IPOB) wato Nnamdi Kanu domin a tada mummunan rikici a arewa da kudancin Nigeria, ba su ci nasara ba aka murkushe yunkurin karen farautarsu Nnamdi Kanu, ya sulale ya gudu suka bashi mafaka a Isra'ila da Ingila, dama yace shi bayahude ne.

To yanzu idan muka lura da kyau ana so ayi amfani da kungiyar shi'ah (IMN) domin a cimma mummunan tanadin da ake burin cimmawa a yankin arewa, kamar yadda akayi yunkuri akan rikin Boko Haram da IPOB, zamu fahimci haka idan mukayi la'akari da irin mutanen da suke magana akan lallai sai gwamnatin shugaba Buhari ta bawa Zakzaky 'yanci.

Matakin farko da suke bi shine, suna duba wanda a cikin al'umma wa zai iya haddasa wa gwamnati matsala, kuma yake da tarin mabiya masu yawa, sai su karfafashi, su bashi 'yanci, su bashi kudi da makami ta boyayyun hanyoyinsu da kuma ta hanyar manyan kungiyoyin su na agaji.

Kuma fa ba wai Zakzaky suke kauna ba har cikin zukatansu, a'ah amfani suke so suyi dashi ba tare da shi din ya sani ba, kamar yadda Muhammad Yusuf ya kasa fahimtar hakan kafin ya shelanta jihadi, su yanzu babban abinda suke so shine ace wani abu ya samu Zakzaky a kurkuku misali ace ya mutu, shikenan sun samu babban hujja tunda dama kotu tace a sakeshi an ki.

Mafita guda biyu ne:
1-Gwamnatin Nigeria ta haramta kungiyar shi'ah (IMN), abi a kame shugabanninsu, a hanasu gudanar da kowani irin taro, idan magoya bayansu suka rasa masu ingizasu to zasu ja da baya, domin duk duniya babu wanda yafi karfin gwamnati sai dai idan kyaleshi akayi saboda wata manufa.

2-Gwamnati ta sakar musu shugaba, a masa daurin talala kamar yadda nayi bayani a sama, amma gwamnati ta kwana da sanin cewa duk ka'idojin da za'a gindaya masa kafin a bada belinsa ba zaiyi biyayya ba, zai karyasu idan an sakeshi, saboda bai yarda da gwamnatin Nigeria ba, musamman yanzu da zuciyarsa ta kara yin tauri a kurkuku.

A cikin abu biyu da na kawo dole gwamnatin Nigeria ta aiwatar da guda daya saboda maslaha ta zaman lafiyar Nigeria, duk da gwamnatin Nigeria tana da karfin iko da zata iya murkushe tarzoman 'yan shi'ah, to amma idan aka lura gwamnati tana fama da yaki da kungiyar Boko Haram, ga barazanan masu garkuwa da mutane, da kuma rikicin fulani makiyaya da manoma, da irin makudan kudi da gwamnati take kashewa, yau idan akace 'yan shi'ah sun dauki makami to fa komai zai tsaya ne a Kasar, zai taba tattalin arzikin Nigeria, jama'ar kasa zasu shiga cikin wahala musamman talakawa.

Cigaba da rike Malam Ibrahim Yakubu Zakzaky duk da umarnin kotu na sakeshi kamar ana bawa magoya bayansa hujjar su cigaba da zanga-zanga ne, ana basu hujjar su nemo taimako koda a gurin manyan kasashen turawa masu kiyayya da cigaban Nigeria ne, kuma ana basu hujja su sadaukar da rayuwarsu ko da ta hanyar daukar makami ne don su kubutar da shugabansu.

Umarnin kotu na a sakeshi shine ya lalata komai akan shirin da gwamnatin Buhari takeyi a kan Zakzaky, tun farko da an hana kotu bada umarnin a sirrance, gwamnatin Buhari bata da wani hujja da zata samu goyon baya, bin umarnin kotu shine maslahar zaman lafiyar Nigeria.

Muna rokon Allah Ya bawa shugabannin mu ikon aikata daidai, Ya tabbatar mana da zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top