Idan kanaso fahimtar labarin koma na farko idan baka karanta na farko ba , ba za'a fahimci komai ba.

 Matata ta biyu mun hadune da ita a cikin jirgin sama ina dawowa daga harkar kasuwamci na ita kuwa a nan kasar take karatun hada magunguna wato Pharmacy a turance. 
Ba kyauta bane ya jawo hankalina ba, a'a, irin dabi'unta da kamakanta dana lura dasu tunda daga filin jirgin har zuwa shiganmu cikin jirgi tana cikin natsuwa tare da girmama mutane cikin mutuntaka sune suka jawo hankalina a kanta.

Kujera daya ya hadamu, wannan shine sanadiyar maganata da ita. Da yake doguwar tafiyace kuma akwai ratsai kamin mu sauka Nijeriya nan take muka saba ta saki jiki dani sosai an an na fahimci gari daya zamu sauka. Nasan unguwarsu, nasan mahaifinta dayake fitatcene a gari.

Bayan mun dawo kamar da makwanni biyu ne na nemi na kawo mata ziyara gidansu tako bani izini. Sai dai amsar data bani a lokacinda na bayyana mata soyayyata shine ya dauremini kai. Domin cemini tayi ta yaba da halina da ace zata auri namiji zata iya aurena.
 Nayi matukar mamakin jin wannan kalmar daga bakinta kuma taki yi mini fassaransa a haka dai na hakura na ci gaba da damunta da zancen aure har sai data amince.

Macece mai matukar kula da addini, tana ganin darajar duk wani nawa. Bata kyamar 'yan uwana musamman wadanda suke zuwa daga kyau. Gata kuma da kyau.
Tafi watanni biyu bata fita ko kofar gidanmu tunda muka dawo daga yawon hutun aure. Sai dai na lura a kullum mata zarara kyawawa suke mana zariya gida, wasu tun muna soyayya nasansu, wasu kuwa sai da mukayi aure. Wasu matan aurene wasu zaurawa ne akwai kuma 'yan mata.
Da yake kowa da bangaren karbar bakinsa bansan safgardasuke ba. Takanzo ta saurareni koda kuwa tana tare da bakinta har sai na fita ko na kwanta na huta ko kuma tanemi izinin komawa wajen bakin nata.

 Tswaon shekara guda ban taba musu da ita ba. Bata taba batamini rai ba. Bazan iya cewa ga laifinta ba a tsawon wannan lokacin. Duk kuwa da ta bude babban shagon saida magunguna a nan kusa da gidanmu tana kuma duba marasa lafiya aikin nan nata bai taba dauke mata hankali wajen kula dani ba. Duk wani abu danake so a lokacin danake so ta sani kuma shi take yi.
Sai dai na fahimci kadaitanta da mata ya soma damuna, duk kuwa da aikinta ko sana'arta yana bukatar hakan ganin yadda ta shahara nan da nan mata har gida suke binta domin neman magani duk kuwa da masu tayata aiki.
Tasha koka mini aka bana gamsar da ita, sau da dama tana nuna mini bacin ranta duk kuwa ina ganin ina matukar kokari. Na aureta tana da shekaru 29 amma tayi mini rantsuwa irin na musulunci babu wani Dan namiji daya taba saninta 'ya mace, banyi mamaki saboda da akwai irinta da dama da Allah Yake tsarewa a maza da mata don haka wannan yasa na kara bata amanna da yarda ba tareda nasan cewa akasarin matan dake zuwa gidan madigo ke kawosu ba. Wasu nan ne mahadarsu saboda sunfi sakewa wasu kuwa 'yan matanta ne zance ko samarinta ke zuwa suna madigo.
Kanwata ta soma ankarar dani, tunma kamin na aureta tace tasan wata kawarta 'yar madugoce don haka ta shawarceni na kara bincike. Ban dauke zancenta da mahimmanci ba, watarana datazo gidan suka hadu da kawar nan ne ta sake mini tunin tafaga wacce tana gidan nan, ban kwabeta ba ban kuma dauki maganan nata da mahimmanci ba.
Wata rana na dawo gida kamar yadda na saba da misalin 9 na dare har aka bude mini kofa naje na ajiye mota na shiga bangarena, nayi wanka na fito banji motsin matata ba. Hakan yasa na kirata a waya yana bugawa ba a amsa har sau uku sai na yanke shawarar na leka bangaren nata, ga wayanta a falo amma babu kowa. Na wuce na duba cikin dakinta dake sama, ina tura kofa sai kawai naga...........
Nashiga tashin hankali matuka a yanayin dana samesu da wacce kanwata take mini magana. Na kasa ce musu komai sai kuka nake yi ina salati ina karanta duk abundant yazo bakina. Ina gani ita wannan tasa kayanta ta fice. Ita kuwa matata sai bani hakuri tana kiran sharrin shadan ne.
Wata zuciya race, na daketa, wata tace na mata saki uku, wata kuwa tace kada nace umfam na koma dakina nayi sallolina na nafila dana saba, kuma wannan shawarar na dauka. Na tashi zan fita ta rike mini riga tana kuka tana neman gafarta ban tanka mata ba, na fizge na kuma mata ishara kadata biyoni.

Tunda na shiga dakina na kulle, saida nayi kwanaki uku ban fito ba. Ta kirani ta aika sakonnin tex ban kulata ba. Sakonta na karshe a daren rana na ukun ne datace idan nan da mintuna 30 bata ganni na sauko na dauki gawanta shine sakon daya kwantar mini da hankali nan take kuma hankalina ya dawo kadata kashe kanta ko kamin ta kashe kanta ta tonawa duniya abunda ya shiga tsakaninmu. Nan take na saka riga na nufi dakinta tana ganina ta sake fashewa da kuka tana na yafemata ta tuba tabi Allah bazata sake aikata wannan abunba. Na rungumota na ce mata mu wuce dakina.
Bayan mun natsune sai yawan kukamini bana gamsar da ita ya fadomini a rai. Na tambayeta ina son ta fadamini gaskiyar abunda yasata aikata wannan danyen abun kuma ina son ta yi mini alkawarin tsakaninta da Allah bazata sake aikatawa ba. Labarin data bani yanada dan tsawo amma kuma Malam Tonga duk darasin da ya kamata maza magidanta da iyaye zasu dauka yana cikin labarinnata wanda shinema kusan dalilin dayasa na rubutu wannnan labarin.
Bayan ta bani hakuri sosai na yadda duk Dan Adam da yayi nadama da kuskure zai iya yi ta kuma yi mini alkawari daga wannan har ta koma ga Allah da ita da madugo har abada sai ta soma da cewa.......

ZAmu ci gaba.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top