Ina matukar mamaki ga wanda ke burin wani abu na rashin lafiya ko wani iftila'i ya samu yan fim su fito su yi ta zagi ba tare da sun bincika ba.
Kai tsaye ina tare da yan fim domin ina rubutu ga wannan masa'anta, sannan a gefe ina da kungiyar da ke tallafawa mabukata wacce ba don taimakon da Yan fim su ka yiwa Moda ba, da ko Gidauniyata ko ta Mansura Isa mu zamu nemar masa taimako, amma kokarin jinyarsa da Yan fim su ka yi ya sanya ba mu yi ba.
Shekaru kusan uku Moda na fama da larura wanda yan fim din ke taimakonsa, su ka hana a sanar a kafafan yada labarai saboda gudun aikata riya, amma kasancewar ciwon na shi diabetes ne dole aka bukaci yanke kafarsa ba don baa kulawa da shi ba sai don ciwon yaci karfinsa, wanda har lokacin dai su ne a tsaye a kansa, kuma har bayan an yanke sun ci gaba da daukar nauyinsa ba tare da sun gayawa duniya suna taimakonsa ba.
Amma daga bayyanar hotonsa a jiya da su dai yan fim din ne su ka yi suna neman addua Yan dadi zagi sun fara tsine musu.
Wato su dai har abada ba za su fita ba, kwanaki da su ke taimakon mabukata muna fada kun ce riya ce, yanzu kuma da su ke yi a boye kun ce ba sa yi.
Kun san cewa yanzu haka Sani Sk ba shi da lafiya Yan fim ne ke dawainiya da shi sun hana mu sanar? Ko kunsan kafin Arrahus ya rasu Yan fim sun yi Gidauniya sun hada masa sama da miliyan guda, ko kunsan lokacin da aka yi garkuwa da wani dan fim sun hada masa kudin da ya taimakawa danginsa gurin fito da shi? Akwai Yan fim ba adadi da ake taimako wanda baa dafada.
Kuma tsahon shekarun da Moda ya yi yana jinya nawa wani ya bayar bayan yan fim?
Daga yanke masa kafa jiya zuwa yau na san manyan yan fim da suka kai masa taimakon kudade da group-group na Yan fim da ke ta kokarin hadawa.
Abun da mu ke bukata kai me zagi Moda musulmine Dan'uwanka, nawa ka tallafa masa da shi tsahon shekarun da yan fim ke masa a boye? Ko me za ka tallafa masa da shi a yanzu bayan zagin wanda ke dawainiya da shi?
Allah ya ba mu ikon yiwa juna nasiha irin yadda Manzon Allah ya yiwa Kafirai har su ka shigo addini ba irin wacce ake a wannan zamanin ta kara fusata mai laifi wanda mun san ba koyarwar addinin Allah ba ce, amin.
©HausaLoaded
Post a Comment