Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Thomas John a matsayin mukaddashin ciyaman na hukumar da ke kula da jagorancin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).

Kamfanin ta bayyana hakan a wani jawabi dauke da sa hannun manajan darakta na NNPC, Dr Maikanti Baru a Abuja, a ranar Talata, 25 ga watan Yuni.

A cewar jawabin, sabon nadin zai fara aiki a nan take.

Jawabin ya bayyana cewa zai riki mukamin har sai an nada sabon Ministan man fetur ko karamin ministan man fetur don fara jagorancin a matsayin Ciyaman.

Jawabin yace hakan yayi daidai da sashi na 1(3) na 2(1) na dokar NNPC.

John, wanda ya kasance tsohon Manajan Darakta na NNPC, ya kasance mamba a kungiyar mahukuntan NNPC.




A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon Shugaban kamfanin NNPC a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni.

Kafin nadin Kyari, ya kasance babban Janar Manaja mai kula da Bangaren Kasuwaci da Cinikin Danyen Mai. Kuma tun daga watan Mayu 2018 aka kara masa matsayi inda ya shi ne Wakilin Najeriya a Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC).

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top