Shugaba majalisar dattawan Najeriya , Ahmed Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa babu wani kudin kirki da yan  majalisar dokokin tarayyar Najeriya  ke samu kamar yadda ake cece-kuce a kai da kuma  zato.  Lawan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin  kungiyar  yan majalisar wato Senator’s Forum a ofishin da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Talata 25 ga watan Yuni 2019,  domin karfafa maganarsa kan albashinsu mara tsoka, Sanata Ahmad Lawan ya cewa, albashin sa da na takwarororinsa sanatoci naira 750,000 ne.
Inda ya  jaddada cewa bai taba  imanin cewa akwai wani kudi mai yawa da ake biyan majalisar dokoki ba.

Yan majalisar dattawa da wakilai na karban albashin su yayinda ni ina karban N750,000 matsayin albashi.

Amma wajibi ne inyi aiki a matsayin sanata, ofishina na bukatar kudi sosai." Ya yi alkawarin cewa babu wani abinda za'a boyewa yan Najeriya game da ayyukan majalisa musamman bangaren kudi.
Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa, bayan albashin da yake karba kowace wata, ana bashi miliyan 13.5 matsayin kudin ayyukan ofis, tafiye-tafiye da dai sauran su. sai dai magana bata yiwa  sanatocin Najeriya dadi ba a wannan  lokacin, duba da cewa basu son duniya ta san abun da suke kar a fili.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top