1. Ki kula da sahar Facebook, ba wajen wasa ba ce da yin abin da aka ga dama.

2. Ki kyautata abin da zaki rubuta a shafinka, ki sani duk abin da kika rubuta zai riqa yawo, zai kai inda baki taba tunani ba, idan kin rubuta alheri sai mabiyanki su yi miki fatan alheri tare da addu'o'i na gari, in kuwa kika rubuta sharri sai mabiyan naki su jefe ki da munanan kalmomi, da duk wani abu da zai sanya ki bakin ciki.

3. Duk lokacin da kika rubuta wani abu a shafinki za a sami wadanda za su qarfafa miki gwiwa, wato ko mummunan abu kika rubuta sai an sami wadanda za su kara miki qaimi, kadan ne daga cikin mabiyanki za su yi miki wa'azi mai kyau da nasiha.

4. Kar ki yarda ki qulla abota da mutanen banza, lallai su mutanen banza suna yin kira ga munanan ayyuka.

5. Idan za ki tura neman abota, kar ki turawa wanda ya sanya sunan batsa da hoton banza a profile dinsa.

6. Kar ki bawa mutanen banza damar hira da ke, da zarar kin fara chat da wani ko wata sai ya fara zancen batsa, ki dakatar da shi. Ki yi masa gargadi a kan ya dena, idan yaqi denawa ki yi maganinsa ta hanyar yin blocking dinsa.

7. Ki koyi yadda ake yin blocking domin kuwa shi ne babban makami na yaqi da duk wani/wata mutumin/mutuniyar banza.

8. Kar ki rudu da abin da wani yake gabatarwa a shafinsa, da yawa daga cikin wadanda ake ganin su mutanen kirki mutanen banza ne, ba za a gane hakan ba har sai an tattauna da su ko an yi hira da su, wato ki tabbatar da nagartar mutum kafin ki qulla abota da shi har takai ga yin hira.

9. Kar ki mayar da shafinki wajen koyar da sharri, ki ji tsoron Allaah Ya ke 'yar uwa mai albarka. Wallahi za a bijiro miki da dukkan abin da kika rubuta Ranar Lahira.

10. Kar ki yi zagi, aibata mutane na gari ko kyarar wanda yayi kuskure. Ki bi hanya mai kyau don yi masa gyara.

11. Ki zama daya daga cikin masu yada ilmin addinin muslunci da na zamani don 'yan uwanki musulmai su amfana. Akwai lada mai yawa da ake samu ta sanadiyyar yada ilmi.

12. Da zarar kin karanta rubutun da yake da muhimmanci ki yada shi, wato ki yi share ko copy don wasu su gani su karanta su amfana.

13. Da zarar kin mayar da shafinki wajen koyar da mutane addininsu, to za su girmama ki, kuma za su riqa ganin mutumcinki.

14. Ki ji tsoron Allaah. Kar ki kirkiri group/page, bayan kin san baki san yadda zaki tafiyar da shi ba.

15. Ki koyi yadda ake kirkirar group/page da yadda ake tafiyar da shi don bashi kariya ta musamman daga mabarnata.

16. Kirkirar group/page abu ne mai sauqi, sai dai tafiyar da shi yana da wahala. Abin sani ki nemi wadanda za su taimaka miki a cikin group/page dinki. Kar ki bawa wadanda ba su cancanci yin rubutu damar yin sa a cikin group/page dinki, ki gayyaci mutane na gari don su koyar da al'umma addinin muslunci a cikin sa.

17. Kar ki yi join/like na group/page din da ake sanya rubututtuka, hotuna da fima-fiman batsa.

18. Ki koyi yadda za ki iya fita daga cikin group din da aka sanya ki, ko yadda zaki dena ganin abubuwan da da ake saki a cikin wani page na banza.

19. Ki zama daya daga cikin masu kiran mutane izuwa ga alheri da kyawawan dabi'u.

20. Kar ki riqa sakin hotunan da kika ga dama a shafinki, in ba haka ba wata rana za a iya jingina zance na qarya a jikinsa. Da zaki yi duba izuwa ga wasu hotuna na 'yan uwanki mata da ake jingina munanan kalmomi, da kin yanke cewa ba zaki taba sakin hotonki a social media ba. Koda zaki saki hotonki ki saki wanda baya bayyana sashin jikinki.

 Abbati Mai Shago Flg
.......✍🏼


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top