Alkali Justice OA Oguwata Na Babbar Kotun Tarayya Dake Zamanta A Gyadi Gyadi Cikin Birnin Kano Yayi Umarni Da Aje Mannewa Hukumar EFCC Kwafin Sammaci Akan Allon Hukumar Dake Nan Kano, Kuma A Dauki Hoton Sammacin Da Aka Manne A Aikawa Da Alkalin, Yin Hakan Tamkar An Sadasu Da Sammacin Da Suka Ki Karba Ne.

Wannan Mataki Ya Biyo Bayan Taurin Kai Da Hukumar EFCC Din Ta Nuna Na Kin Karbar Sammacin Kotu Har Sau Uku, Domin Su Bayyana Hakikanin Gaskiya Akan Binciken Da Hukumar EFCC Din Tace Tayi Na Fefen Bidiyon  Zargin Karbar Rashawa Da Aka Nuna Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Yana Karba, Koda Yake Mai Girma Gwamna Ya Musanta.

Amma Fitaccen Lauya Nan Barr. Audu Bulama Bukarti Shine Yayi Karar Hukumar Ta EFCC Da Shugabanta Ibrahim Magu, Akan Kotun Tirsasawa Magun Daya Fitar Da sahihin Binciken Da Yayi Akan Wancan Fefen Bidiyo. A Zaman Da Kotun Tayi Jiya laraba Barr. Abba Hikima Fagge Ya Bukaci Kotu Ta Amince A Manne Sammacin Domin Sau Uku Ana Kaiwa EFCC Tana Kin Karba, Kuma Idan Ba'ai Haka Ba Tofa Zai Zama Kotu Bata Da Hurumi Kenan.

A Karshe Mai Shari'a Oguwata Ya Amince Tare Da Yin Izini Da Aje A Manne Sammacin, Sannan A Dawo Ranar 8 Ga Watan October Bayan Alkalai Sun Dawo Daga Hutu. Kunshin Bukatar Masu Kara Ya Bukaci Da A Mika Ibrahim Magu Shugaban EFCC A Kurkuku Matukar Ya Gaza Yin Bayani Akan Wancan Fefen Bidiyo.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top