Yan Najeriya sun sako gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a gaba a shafukan sada zumunta tare da kiraye-kirayen a kori wasu na gaba-gaba a gwamnatinsa.
Mutane da dama ne suka yi ta bayyana ra'ayoyinsu a Twitter, inda suke kira  kan a kori Abba Kyari shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa daga mukaminsa da kuma Mamman Daura.

Mamman Daura dan uwa ne na kusa ga shugaban - Buhari inda ya kasance baffansa, duk da cewa ba shi da mukami a gwamnatin amma ana hasashen cewa yana da fada-a-ji a fadar ta shugaban kasa.
Wannan ya biyo bayan wata zanga-zangar da wasu matasan yan jam'iyyar APC mai mulki suka yi domin neman shugaban da ka da ya sake nada ministocin da suka ce sun "hana ruwa gudu a wa'adinsa na farko.

Sannan kuma sun yi zargin cewa ministocin "ba sa son talaka, kuma ba su da gaskiya.
Sanata Shehu Sani ma ba a bar shi a baya ba, inda ya tofa albarkacin bakinsa a Twitter yana cewa:
Wannan zanga-zanga ana yi ne tsakanin 'yan tsirari masu fada-a-ji na fadar shugaban kasa da kuma gungun matasa domin neman iko a fadar gwamnati.

Wasu da dama sun saka hotunansu a wurin zanga-zangar da suka yi suna yin zambo da ba'a da sauran kalamai iri-iri kan Abba Kyari, Shugaba Buhari da Mamman Daura.
@lifeinarewa ya ce, yan Najeriya ba Abba Kyari suka zaba ba, ba kuma Mamman Daura ba.

Sai dai tuni mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya gaya wa BBC cewa wasu masu neman mukami ne suka debo mutane domin yin zanga-zangar.
Wasu sun sa ido kan wadannan mukamai saboda wasu bukatu nasu na daban, in ji shi.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top