- Ya ce babu yadda za ayi duk hadisan da suka sunnartar da azumin, haka kawai dare daya wani ya zo ya karyata su
- Malamin ya kawo lambobin hadisai da dama da suke nuni da hallacin yin azumin sittu shawwal
Shahararren malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano, kuma limamin Masallacin Sahaba, Sheikh Muhammad Bin Uthman, ya ce duk wani mutumi da ya fito ya ce azumin 'Sittu Shawwal' bidi'a ne, ya fada ne kawai saboda jahilci, shubha ko kuma neman suna.
Jaridar Dabo FM ita ce ta binciko karatun malamin wanda yayi ranar Juma'a 14 ga watan Yuni, 2019, a masallacin da Sahaba wanda yake limanic dake unguwar Kundila a jihar Kano.
Malamin yayi ta karanto jerin Hadisai da lambobinsu, wadanda suke nuni da cewa azimun sittu shawwal sunna ne.
"Musulim ya ruwaito hadisi na 1,164, Abu Dawud a cikin sunan mai lamba 2,433, Imam Tirmidhi 759, Ibn Majah hadisi na 1,706, da Ahmad Bin Hambal ya ruwaito hadisai masu lamba 23,534, 23,556, da kuma 23,561."
Shahararren malamin ya ce jahilci ne karara ga wani jahili ya zo yace wai azumin sittu shawwal bidi'a ne, ya kara da cewa a cikin littafin Abdurrahman bin Muhammad, mai suna Al Ihkam Shar Usulil Ahkam an ruwaito hadisi mai dauke da sunnancin yin azumin sittu shawwal.
"Ashe kenan jahilci ne ga wani jahili ya fito ya ce azumin sittu shawwal bidi'a ne."
"Mun yi wannan magana ne saboda an yiwa sunnar Manzon Allah rashin kunya, saboda haka yasa muke kausasa harshen mu ga wannan jahilin (Dr Ahmad Gumi), domin kusan da wannan."
"Hakan ba shine muka san abinda (Sheikh Malam Abubakar Gumi) ya rasu ya bari akan a koyar da addinin musulunci ba."
"Amma saboda rashin kunya da son zuciya kawai wani ya fito ya ce wai wadannan hadisai sune Imam Malik ya zuba a bola."
©HausaLoaded
Post a Comment