Idan ka daki matarka ta aure riban me zaka samu kuma dadin me zakaji, wani cigaba zaka samu?

Idan kaji labarin mijin mahaifiyarka ( mahaifinka ko wanda ba shi ya haifeka ba) ya daki mahaifiyarka ya zakaji a ranka?

Idan ka aurar da 'yar ka ma wani sai ya mata dukan tsiya ka samu labari shin zaka kwana cikin farin ciki an daki 'yarka?

Idan mijin kanwarka ko yayarka ya mata dukan tsiya tsakani da Allah zakaji dadi?

Matarka da kake duka mahaifiyar 'ya'yanka ne, kanwar wasu ne, yayar wasu ne, kuma 'yar wasu ne, abinda ba zakaji dadi idan an maka ba to bai kamata ka yiwa wani ba

Mafi girman wulakanci da ban takaici shine magidanci ya yiwa matarshi dukan tsiya akan idon 'ya'yanta, kana tunanin 'ya'yanka zasu taso su ji tausayinka?

To ba duka ba; duk wanda yake cin mutuncin matarshi musamman a gaban 'ya'yanta to yayi babban asara a rayuwa, haka 'ya'yanka zasu taso ba zasu taba jin tausayinka ba, kuma ba zasu taimake ba saboda cin mutuncin mahaifiyarsu da ka yi akan idon su

A matsayina na wanda yake da mata, banga abin duka a jikin mace ba, Allah bai halicci mace don a daketa ba, ina Allah wadai da duk wanda yake dukar matarshi na sunnah

'Yan mata ku lura da kyau, kuma ku nutsu, kar zakin bakin samarin zamani ya rude ku, ba auren ba zaman auren shine babban abin lura, ku kiyayi auren wadanda sha'awarku suke ba kauna hadi da tausayawa ba, ku bi umarnin Allah, kuyi hakuri ku kiyaye dokokin Allah, insha Allahu Allah ba zai hadaku da mugayen mazajen aure ba

Allah Ka shiga tsakanin mata musulmi da mugayen mazaje Amin


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top