Ina kuma muku addua Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya. Wani aboki na yake sanar da ni wannan labari, kuma wannan labari da gaske ne. Wasu mutane sun zo wajen wani mutum wanda yake shi dila ne na sayar da motoci a wajen sana’arsa, sai suka yi cinikin wata mota kirar Camry, a kan kimanin kudi naira miliyan biyar. Sai suka karbi lambar asusun bnkisa a kan za su yi masa transfer na kudin, sai ga naira miliyan uku sun shigo cikin asusun banki na mutumin, a kan za su ciko masa sauran kudin daga baya. 

Bayan wani lokaci sai suka zo suka ba shi hakuri a kan ba za su iya sayen motar ba, saboda rashin kudin da za su cika, sai suka ce to ya ba su miliyan biyu da dubu dari biyar, sun ba shi saura naira budu dari biyar din saboda dawainiyar da ya yi musu. Wannan mutum yana murna ya samu na banza.

 Bayan kwana uku yana zaune a wajen sayar da motocinsa sai ga jami’an rundunar yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane da sun zo suna tambayar sa ko shi ne aka tura masa miliyan uku, ya ce eh? Kuma shi bai san su ba, bai taba ganin su ba. To wata hanya ce ta masu garkuwa da mutane suke yi wajen amsar kudin fansa daga yanuwan wadanda suka kama. Dan Allah a yada wannan a sanar da yanuwa a yi yekuwa a masallatai da dukkan wurare da ma gidajen radiyo da makarantu.

 Haka nan ka da ku yarda ko da danuwan ka ne ya nemi ka ba shi lambar asusunka ba tare da ka bincike shi ba. Kuma idan wani amini gare ka ya bukaci zai tura maka kudi ko za a tura masa kudi, idan ka ga kudi ne masu yawa, to ku yi rahoto a ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin kada wani tarko ne ba ka sani ba. 

Sako daga Dakta Mansur Ibrahim, Sakkwato




© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top