Ga duk wanda ya ke kallon shirin Kwana Casa'in, ya san cewa Surayya Aminu wadda a ka fi sani da Rayya tauraruwar ta na haskawa a cikin shirin kasancewar matsayin ta a ciki shirin na fitowa a munafuka da kuma mai wauta wanda hakan ya sanya ta yi suna sosai.

Majiyar mu ta Northflix ta sami damar tattaunawa da jaruma Rayya, wato Surayya Aminu mu ka ji ta bakin ta in da ta fara da tarihin rayuwar ta kamar haka.

"Ni suna na Surayya Aminu, kuma an haife ni ne a garin Ikeja da ke jihar Legas, amma na girma ne a jihar Kaduna, na yi karatun firamare da Sakandare da na Islamiyya duk a garin Kaduna. A yanzu kuma ina karatun Digiri a Jami'ar Karatu daga gida wato (NOUN)”.

Dangane da yadda ta samu kan ta kuwa a matsayin jaruma cewa ta yi "To ni dai tun ina karama na ke da burin na ga na yi harkar fim, amma dai abin da ya ba ni karfin gwiwar shiga shi ne saboda ina so na ga na karanta Mass Communication wato karatun koyon aikin jarida, to wannan burin kusan dai shi ne abin da ya ja ra'ayi na wajen shiga harkar fim. Kuma wanda ya yi mini hanyar shigowa shi ne Nura M, Sultan a nan Kano da kuma Nazir Adam Saleh, wadannan su ne su ka zama hanya ta ta shigowa harkar fim".

Daga lokacin da Surayya ta shigo harkar fim zuwa yanzu ko ta yi fina-finai kamar nawa?

"To fina-finan da na yi ba su da yawa, domin ban dade da shigowa harkar ba, amma duk da haka fina-finan da na yi za su kai biyar, kuma a yanzu da za a tambaye ni wanda na fi so a cikin su to gaskiya na fi son Kwana Casa'in, saboda shi ne Duniya ta sanni, don haka na fi son sa a cikin dukkan fina-finan da na yi. Don gaskiya na ji dadi sosai da na samu kaina a cikin shirin Kwana Casa'in, kuma na ji dadin irin fitowar da na ke yi irin ta munafurci da rawar kai da sauran su domin hakan ina jin dadin fitowa da na ke a cikin wannan shirin babu abun da zan ce sai godiya ga Allah ".

Ko jaruma Surayya akwai wata jaruma da ta ke burge ta kuma ta ke koyi da ita a salon fim?

“'A gaskiya ni babu wata jaruma da na ke koyi da ita, kawai dai ana ba ni role ne, ni kuma ina hawa, don haka ba maganar koyi da wata ba ne." inji Rayya.

Daga karshe ko wanne buri Surayya ta ke da shi?

Sai ta karkare zancen ta da cewa "Buri na dai na samu shiga duniya ta sanni, kuma a yanzu Alhamdulillahi babu abun da zan ce sai godiya ga Allah, kuma ina godiya ga wadanda su ka yi min hanya, sannan masoya na ina yi musu fatan alheri, Allah ya bar mu tare." A cewar jaruma Rayya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top