A yau filin namu ya yi waiwaye ne game da hadarin sanya hotunan da aka ga dama a duniyar shafukan walwalar jama’a da suka kunshi facebook, twitter, instagram, snapchat da dai sauransu. 


A halin yanzu, harkar duniya ta yi nisa a zukatan al’umma har ya zamto mata da maza kowa ba ya jin kunyar saka kowanne irin hoto a kan kafar sadarwa ta zamani irin su, facebook da Instagram. 

Wannan masifar tafi kamari a wajen matasan mata har matan aure ba a barsu a baya ba.

 Mace za ta dauki hoto ko da hijab ko mayafi babu a jikinta, hasali ma a jikin hoton sai ta fito da boyayyun abubuwan da Allah ya haramta bayyanar da su, sannan ta watsa ma duniyar facebook ko instagram.

 Ta aikata laifi biyu, daukan hoto da kuma yada sharri da fitina. Nan take sai fasikan samari su fara yin sharhi suna yabon siffar jikinta, suna bayyana sha’awarsu gareta, ita kuma shaidan yana kara zuga ta tana jin cewa ashe ita kyakkyawa ce. 

To inda matsalar take shi ne, akwai abin da a addinance ake kiransa da suna “kambun ido”, wanda kamar yadda malamai ke yin bayani wani irin karfi ne na mugunta wanda yake boye a cikin zukatan wasu daga cikin mutane da aljanu, wanda a cikinsa akwai wani karfi dake cutarwa ga duk wanda aka nufa da shi. 

Masu irin wannan abu suna nan da yawa a cikin al’umma kuma ba gane su ake yi ba, balle a kiyaye. Suna nan tun kafin zuwan Annabi Muhammadu (SAW), kuma har shi kansa ya yi magana sosai game da su, kuma yana neman tsari daga sharrinsu. Ya ce, “bayan kudurar Allah (SWT) babu abin da ke kashe yawancin al’ummata fiye da kambun ido”. 

Tasirin muguntar kambun ido ya zarce na aljani ko na matsafi. Kuma ya fi su wuyar magancewa. Su kansu aljanu suna tsoron mai kambun ido a cikin su ko a cikin mutane.

 Binciken malamai ya tabbatar da cewa kambun ido ko kambun baka su kan yi tasiri ne a duk lokacin da masu ita suka nufi hassada a kan mutum ko suka ji haushin mutum ko wani abu nashi, ko makamantan haka. To illar a nan ita ce, yayin da kika dauki hoton fuskarki ko gaba daga jikinki kika tura a kafar sadarwa, to za ta yiwu a cikin masu yabon siffar halittar taki akwai masu irin wannan kambun ido ko na kambun baka, wanda nau’i ne daga cikin nau’uka na maita.

 Suna ta yabon siffarki kina jin dadi, kwana kadan kuma ki fara samun matsaloli a lafiyar jikinki ko a zaman aurenki, ko a kan harkar karatunki ko kuma duk abin da kika sa a gabanki ki ga babu nasara.

 Watakil ki fara zargin ko kishiyar mamanki ce ta yi miki asiri, ko wani tsohon saurayinki ne yake bin ki da sharri ko wata kawarki, alhali kuwa duk ba haka ba ne.

 Kin hadu da masu kambun ido ne, ke ce kika jawo ma kanki matsala. Kin ga ke nan bayan zunubin laifin bayyanar da tsaraicinki ko siffar jikinki, to ga kuma na kambun ido ya dabaibaye ki, sannan kuma ya dabaibaye rayuwarki. 

Abin tausayi kuma sai ka ga wasu har hotunan yara kanana da jarirai suke sanyawa, sun ja ma kansu, sun ja ma ‘ya’yansu.

 Ko kun san cewa masu kambun ido ko da ba su taba ganin ka ba, idan wani ya siffanta musu kamanninka za su iya kama ka? Amma ba karfin kambin ido ko kambun baka ne ke tasiri da kan shi ba kadai, a’a sai da ikon Allah da kaddarawarsa, domin babu abun da ke faruwa sai idan Allah Ya kaddari faruwar sa, dan haka wajibi ne mu kiyaye domin Allah Ya kiyaye mu. Ya Allah ka shirye mu ka gyara dukkan lamuranmu daga fitinar fili da ta boye, ka kiyaye mu daga sharrin shaidanu da masu kambun ido.



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top