Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ce Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba zai hana hukumar yaki da rashawa ta EFCC daga bincikarsa ba.
Mai Shari’a Binta Nyako ta sanar da hakan ne yayin yanke hukunci a ranar Juma’a, a kan karar da gwamnan ya shigar.
Gwamnan na bukatar jin matsayar kotun ne a kan ko ya bi dokar majalisar zartarwar tarayya a yayin siyar da gidajen gwamnatin tarayyar da yayi a tsakanin watan Mayun 2005 zuwa Mayun 2007 a lokacin da yake ministan Abuja.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a yayin da El-Rufai ya maka EFCC, ministan FCT, FCDA, AGF, babban bankin Najeriya, Bankin Oceanic, Bankin Access, Bankin Intercontinental, Aso Savings and Loans Ltd, Union Homes, Akintola Williams Deloite da Aminu Ibrahim & Co gaban kotun tarayyar.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, mai shari’a Binta Nyako din ta amsa bukatun da gwamnan ya miko gaban babbar kotun tarayyar a kan wadanda yake kara.
Amma kuma, a hukuncinta na ranar Juma’a, mai shari’ar ta bayyana yadda hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta garzayo kotun da bukatar da ke suka ga bukatun gwamnan.
Hukumar yaki da rashawar, ta ce take-taken gwamnan shine samun kariya daga binciken da hukumar za ta yi a kansa.
Yayi hakan ne don rufe zargin almundahanar da ake zarginsa da yi ne a yayin da yake Ministan Abuja.
Jastis Nyako, ta janye tsohon hukuncinta inda tace babu kotun da za ta hana hukumar yaki da rashawar bincikar kowa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tabbatar.
“Babu kotu, har da wannan, da za ta bari a yi amfani da ita don zama kariya daga binciken EFCC,” ta yanke hukunci.
Ana zargin gwamnan ne da badakalar wasu makudan kudade ne a lokacin da ya yi ministan birnin tarayya.
Ana zarginsa da sayar da wasu gidajen gwamnatin tarayya tsakanin watan Mayu 2005 zuwa watan Mayun 2007. Amma kudin sun yi batan dabo ko layar zana.
Post a Comment