Madallah da wannan sharshi, daga Chairman Hamisu @iyantama
Ina godiya sosai. Allah ya bar zumunci.

Wannan Shiri Almara ne.

Fim din yayi nuni da tsantsar Imani da yarda da Allah akan komai.
Tunda har Allah yayi halittar  sammai da kasssai da abunda ke cikin su toh kar ka sake kayi tantama idan akazo maka da wata magana data shafi iko irin na Allah.
Wannan fim yayi kokarin zakula Isa irinta Allah subhanahu wata, ala.

A cikin shirin anyi nusarwa mai girma ta yadda ya kamata mutum ya girmama duk wata halitta da zai iya haduwa da ita wadda ka sani da wadda baka sani ba. Girmama halittun Allah nada muhimmanci.

Fim din ya nusar da masu kallo cewa raina halittar Allah ka iya kawo maka musiba da bakayi zato a rayuwa ba.
Allah yana da ikon halittar dan Adam ta yadda yaso hala mutum mai kusunbi ko mutum da kawuna 2 ko kai 3,gurgu ko makaho koda yatsu ko babu.

Fim din ya hanemu da rainuwa da kaskanta halittun Allah.

"Wannan shiri sai da ya tunamin da Tarihin Ashabul kahfi."

Anyi amfani da kayan aiki masu kyau,Jarumai kwararru na da dana yanzu da kuma sabbi.
Kamfanin da suka shirya sunyi kokarin samar da duk abubuwan bukata domin Inganta shirin.

Ma,aikatan shirin sunyi kokari mutaka gaya.

Wanda ya bada umarni Falalau Dorayi  yayi wasa da
kwakwalwar masu kallo sosai.

 Na samu  jin nishadi lokacin danake kallon fim din saboda akwai barkwanci cikin hotuna da kuma kalma.
Hakika wannan shiri yayi.

Duk wanda ya kalla  ba zaiyi asarar kudin sa ba ko kuma yayi danasanin shiga kallon ba. 

Wannan Sharhi Ra,ayi nane da fahimta ga fim din saboda haka kowa nada nasa ra ayin.#
Iyantama

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top