by Naziru Dalha :

 Ana yawan cewa aure ba na yara bane. Tabbas ba na yara bane amma na mutane ne masu alkibla wadanda suke kaunar juna kuma suke da burin kasancewa tare har abada. 

Auren wuri na da amfani masu tarin yawa. Ga kadan daga cikin amfanin auren wuri ga ma’auratan. 

1. Ma’aurata zasu girma tare Idan matasa biyu suka yi aure, akwai yuwuwar su taso tare cike da fahimtar juna da kauna mai tarin yawa har zuwa manyancensu.

2. Ba a cika saka manyan burika ga juna Idan masoya suka yi auren wuri, basu cika saka burika masu yawa a rayuwarsu ba. Kullum fatansu shine gina rayuwar aure mai kyau tare da taso da yara nagari. 

3. Ma’auratan ka saba morar junansu Sakamakon rashin manyan burika a rayuwa, su kan saba da morar komai na juna. Suna mayar da kayan juna nasu ne. 

4. Biki wanda bai cika da karya ba Sakamakon rashin girman ma’auratan, su kan kwantar da hankali ba tare da sun saka karya ba a yayin shagalin bikinsu. 

5. Halayyar amfana da kayayyakin juna Sakamakon auren wuri, ma’aurata kan saki jiki da juna har su dinga daukar kayayyakin juna suna amfana da ita. 

6. Akwai rayuwa mai matukar tsawo Fara zaman auratayya da wuri kan ba ma’auratan damar doguwar rayuwa tare. Su kan samu isasshen lokacin da zasu zauna har muddin rai. 

7. Ma’auratan kan dandana rayuwar manya tun da wuri Aure kamar yadda wasu suke kallonsa, rayuwa ce ta manya. Auren wuri kuwa na sa ma’auratan su fara dandanar rayuwar manya ta hanyar zama iyaye da wuri. 

8. Ma’auratan kan zauna cikin farinciki Auren wuri na kawo natsuwa da cikar kamala wadanda sune jigo na samuwar farin ciki. 

9. Akwai isasshen lokacin rayuwar auren ko kuma kara wani auren idan rabuwa ta gibta Sakamakon auren wuri, ma’auratan da suka rabu da juna kan kara yin aure da yarintarsu. Basu yi tsufan da zasu ce an hakura da juna. 

10. Babu hatsari mai yawa tattare da daukar ciki Mace mai shekaru 24 zuwa 26 bata tattare da hatsari a yayin da ta samu juna biyu kamar mace mai shekaru 35 zuwa 45.

 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top