Manya-manyan kura-kurai da ma'aurata ke yi ba su sani ba:


Posted by Ayeesh Chuchu 

Rayuwa da Zamantakewa - #matsalar ma'aurata #matsalolin aure #nasiha ga mata #kura-kurai - 


Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. 

A wannan zamani da mu ke ciki, aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa ya ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. 

Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar sa. 

 Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai su iske abun ba haka bane. 

Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita cikinta. 

Akwai kura-kurai da ma'aurata kan aikata wadanda ke jawo matsaloli a rayuwar aure, wanda wasu basu dauke su a bakin komai ba, daga karshe kuma kan iya jawo mutuwar aure.

Daukar juna ba a bakin komai ba 
Da yawan ma'aurata ganin an kwana biyu tare, an saba da juna sai ya zama kar ta san kar ne, su kan manta da abubuwan da kan kara ma zamantakewar su armashi. 

Zai zamo mace duk abinda mijinta zai yi ba za ta ga bajintar shi ba, tana ganin ai dolen shine dan haka ba ta ga abin yabawa ba. Haka ta bangaren maza ma, babu wannan yabawar tsakaninsu da matansu.

Yana da kyau komin kankantar abu da miji ko mata ta/ya yi, a yaba a kuma gode. Hakan zai kara karfafa wa mutum. Idan girki tayi, kamata yayi ka gode ma ta, tare da kwarzanta abincinta, haka bangaren kwalliya ma. Shiyasa wasu matan da sunyi aure, duk wata kwalliya sai su zubar saboda mazajensu ba sa yabawa. 

Haka ta bangaren hidimar gida, ya kamata mata su rika yabawa mazajensu duk da cewa hakkinsu ne su dauki nauyin iyalansu, amma yana da kyau a gode mu su. Hakan zai kara mu su karfin gwiwa.


Dogon buri 
Da yawan maza da mata kan shiga gidajen auren su da dogon buri, suna tunanin babu komai a cikin rayuwar aure face jin dadi. Sun dauka irin rayuwar fina-finai ce da abubuwa na jin dadi da suke gani. Sai dai kash, rayuwa ce mai tattare da kalubale, wata rana zuma wata rana madaci.

Dogon burin da ake shiga da shi na daga cikin manyan kura-kurai da ma'aurata ke tafkawa. Sai bayan an shiga a ga akasin abinda ake tsammani, wanda wasu idan an yi sa'a su kan yi hakuri da abinda suka iske, wasu kuwa a lokacin ne fitintinu za su yi ta bullowa. 

Ya zama wajibi ga ma'aurata su cire dogon buri a rayuwar aurensu, su rungumi abinda suka tarar da hannu biyu da yaƙinin cewa canji na faruwa ne daga kan mutum, sannan daya ya yi adapting da canjin. 

Kasancewar aboki ko abokiyar rayuwar da wani nakasu a rayuwa ba shi ke nuna cewa rayuwar zamantakewa ta ruguje ba. Kowane dan adam tara yake bai cika goma ba. Haka kowane rayuwar aure bai cika dari bisa dari ba, dole a samu tawaya ta wani bangaren. 

Rashin hakuri 
Gaba daya rayuwar aure yar hakuri ce, sannan hakuri shine ribar zaman duniya. 

Muna cikin wani zamani da ma'aurata kamar jiran juna su ke, kowane a wuya yake danuwarsa ya yi abu ya zama abin fada da cece-kuce. 

Kowane ma'aurata suna samun sabani a tsakanin junansu, sai dai mi? Wasu kan yi kokari wajen ganin sun gano bakin zare ta hanyar warware matsalolinsu ta hanyar lumana. 

Wasu kuwa a lokacin ne zage-zage, buge-buge da bakaken maganganu ke kunno kai. Daga nan sai wutar ta kara ruruwa, har ta kai ga abinda ba a so. 

Wasu ma'auratan koda su ne da laifi ya kan zama abu mai matukar wahala su bude baki su bada hakuri. Daga nan sai gardama ta biyo baya. Ko dan zaman lafiya bada hakuri na kashe wutar fitina.

Mantawa da yanda za a so juna
 Daga zarar anyi aure, duk soyayyar da aka tafka a baya sai ta zama tarihi. Babu sauran soyayya da an yi aure komai ya zama tarihi.

Yana daya daga cikin kura-kuran da ma'aurata ke yi, bayan aure ne ya kamata a ce soyayya ta kara karfafa, ba kafin aure ba.

Kowane bangaren mace ko namiji suna da tasu matsalolin. Duk auren da babu soyayya a cikin sa to lallai yana cikin halin rayuwa ko mutuwa.

Rayuwar aure ce ya kamata a kawata ta da duk wasu kalaman soyayya, kulawa da kyautatawa, sai dai akasin da ake samu na komi ya zama tarihi. Yana daya daga cikin kura-kurai dake kawo mutuwar aure.



Sako wasu cikin al'amuran ku
Shigowa da wasu mutane cikin matsalolin aure yana daya daga cikin ababen da ke jawo matsala a rayuwar aure. Wasu ma'auratan na da dabi'ar kai kukan abokan zaman su ga wasu, wala Allah abokai ne, yan uwa ko iyaye a kan abinda bai taka kara ya karya ba.

Irin hakan na rusa aure gaba dayan shi, saboda wadanda ka kai wa karar da irin tunaninsu a kan matsalar da kuke fuskanta.

Shigowar "third party" a zamantakewa na kawo mutuwar aure.

Akwai matsalolin da zama daya za ku yi ku warware matsalarku ba tare da wani ya ji ko ya gani ba. Hakan zai taimaka wajen kawo karshen wasu matsalolin.

Ya kamata ma'aurata su koyi warware matsalolinsu a tsakanin su ba tare da sun fitar da shi waje ba. Hakan zai kara mu su kusanci a Tsakani saboda sun dau juna a matsayin abokai da za su iya zama su tattauna matsalolinsu, sannan su kuma san hanyoyin warware su ba tare da wani ko wata ya shigo cikin lamarin auren ku.

Rashin ba ma juna lokaci 

Daga zarar anyi aure an fara tara iyali kowa ta kanshi yake babu wani sauran bama juna lokaci. Irin wannan ya fi faruwa ga mata, lokacinsu kacokam na yaransu ne. Miji da yayi magana za su yi korafin kula da yara da kuma aikace-aikacen gida.

Wasu mazan kuwa aikinsu ya fiye mu su zama da iyalansu har ta kai su na dawowa da aikin office gida.

Daga an gama an gaji sai bacci, babu wani lokaci da ma'auratan suka ware dan tattaunawa da kuma kara kusanci da junansu.

Hakan na saurin kashe aure, sai ka ji mata na maganar "zaman yarana nake, zaman hakuri nake".

Yanke hukunci ba tare da jin ta bakin daya bangaren ba
Yarda da juna ta sa kuka aminta da junanku a karkashin inuwa daya, babban kuskure daya bangare ya yanke hukunci ba tare da jin ta bakin dayan ba. Shawara na da dadi musamman ma ga ma'aurata, ya kamata su rika shawartar junansu wajen zartar da harkokin rayuwarsu.

Hakan zai sa miji ko mata ganin an girmama su, tunda har za a nemi shawara a wajen su. Hakan na nuna tsantsar yarda da aminta da juna.

Rashin yin hakan ka iya jawo zargi ko wasiwasi a zuciyar daya, ganin kamar babu yarda a tsakani.

Rashin nuna gaskiya
Wannan na daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar aure a wannan zamanin, duba da shigowar kafofin sada zumunta da za a samu har matan aure nayi.

Ba kowane namiji bane kan aminta matar shi ta shiga Social media ba. Haka mata ma kullum cikin zargin mazajensu suke a dalilin hakan.

Babban abinda zamantakewarsu ta rasa shine rashin gaskiya. Idan har kun gini soyayyarku akan gaskiya da wuya irin wadannan ababen su jawo maku fitina a rayuwar aurenku.

Ko ina namiji ko mace zasu kasance kowane bangare na yi wa dan uwanshi kyakkyawar zato. Rashin hakan ya kawo silar mutuwar aurarraki da dama. Duk abinda ma'aurata zasu yi, su yi shi a kan gaskiya da kuma rikon amana.

Rashin tsayawa juna
A duk inda ma'aurata suke ya kamata su tsayawa junansu komin wuya komin dadi. Su zama kafadar jingina ga junansu wajen share hawayen junansu, sai dai mi? Wasu in dai matsala ko damuwa ba tasu ba ce ba, to hakan bai dame su ba, wannan halin ko in kula da su ke nunawa juna na kashe karsashin soyayya, sai ya zama idan shawara ko wata matsala suke ciki maimakon su tuntubi juna sai su kai damuwar su wani waje daban.
Kwatantawa kowa muhallinsa
Wasu kan yi kuskure barin kowa na tsoma baki a rayuwar aurensu. Misali mijin da zai rika bari abokan shi na tsara mi shi yanda zai tafiyar da gidanshi, ko mace kawayenta su tsara ma ta, koma iyaye su rika tsoma baki a rayuwar yaransu.

Miji ko mata dole ne ku nunawa kowanne matsayinsa a rayuwarku da irin muhimmancin da yake da shi, gudun kawo hargitsi a rayuwar aurenku.

Amma matukar aka bar kowa na tsoma baki hakan ba karamin tasiri yake wajen wargaza zaman lafiyar ma'aurata ba.

Daga karshe, za mu iya cewa wadannan suna daga cikin manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi. Ba kuma sukenan ba. I


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top