FITACCEN mawaƙi Dauda Kahutu (Rarara) ya kawo ƙarshen rigimar da ta ɓarke tsakanin wasu mawaƙan siyasa da wasu muƙarraban gwamnan Jihar Kebbi.

A cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata ne wata ƙungiyar mawaƙa mai suna ''Naff Entertainment" wadda aka fi sani da "Mawaƙan APC na Jihar Kebbi" su ka saki wata sabuwar waƙar su mai suna "Jirgin Yawo".

Aƙalla mawaƙa 18 ne su ka yi gamayya su ka rera ta.

Sun yi waƙar ne a kan siyasar jihar, sannan kuma ta yi matuƙar tasiri a jihar inda ta riƙa ci kamar wutar bazara.

Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin Arewa da waƙar siyasa ta fi kowace tasiri a wurin masu sauraro.

Ba a daɗe da sakin waƙar ba sai aka samu labarin cewa wasu mutane waɗanda ba a san ko su wanene ba sun tare wasu mutum biyar daga cikin waɗanda su ka yi waƙar, su ka yi masu bugun kawo wuƙa.

An riƙa yaɗa hotunan su jina-jina a shafukan Instagram.

Mawaƙan da aka buga ɗin su ne Bello Aljanare, Kabiru A. Sani, Musa Alee, Shamsu Otono, da Ayuba Ibrahim.

Lamarin ya sa har sai da ta kai wasu daga cikin fitattun mawaƙa da ke wajen jihar, irin su Aminu Alan Waƙa da El-Mu'az Ibrahim Birniwa su ka fito a shafukan su na soshiyal midiya su ka nuna rashin jin daɗin su a kan cin mutuncin da aka yi wa 'yan'uwan su mawaƙa.

Haka zalika sun bayyana cewa sai sun bi kadin cin mutuncin da aka yi wa mawaƙan Kebbin.

Daga nan kuma sai aka riƙa yaɗa labarin cewar ana neman dukkan mawaƙan da su ka yi waƙar ruwa a jallo, wanda hakan ya sa wasu daga cikin su su ka yi layar zana, aka rasa inda su ke.

Ana cikin wannan sa toka-sa-katsin sai kuma aka samu labarin an gurfanar da uku daga cikin waɗanda su ka yi waƙar a kotu,  har ma an tura su gidan yari, sakamakon zargin sun ci mutuncin wasu mutane a cikin waƙar.

Mawaƙan su ne Ibrahim S. Fulani, Muhammad Sani, da Musa Na'Allah.

Da ya ke yi wa mujallar Fim ƙarin bayani game da sabuwar waƙar, shugaban ƙungiyar mawaƙan, Nafi'u Umar,  ya bayyana cewa wannan waƙa ba ta da nasaba da kowa, riga ba wuya ce, domin ba su kama sunan kowa ba, kawai dai hannun-ka-mai-sanda ne su ka yi, wasu su ka tsargu.

Ana cikin haka ne, a jiya Asabar, 11 ga Janairu, 2020, sai Rarara ya tashi takanas ta Kano ya dira a Birnin Kebbi inda ya gana da Gwamnan jihar, Alhaji Atiku Bagudu, a kan lamarin mawaƙan.

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida wa mujallar Fim cewa gwamnan ya bayyana wa Rarara dukkan yadda dambarwar ta faru, ya na mai cewa bai san ana yi ba.

Fimmagazine na ruwaito,Haka kuma ya ce bai san an yi ƙara ba, bugu da ƙari ma ba ya da masaniya kan waɗanda aka kulle.

Bugudu ya ci gaba da bayyana wa su Rarara cewa ai dukkan mawaƙan Jihar Kebbi 'ya'yan sa ne, sannan idan ma an same su da laifin sun yi masa wani abu wanda bai dace ba, to ya yafe masu.

A yanzu haka dai ana sa ran idan Allah ya kai mu gobe Litinin za a saki mawaƙan da aka kama sakamakon zuwan Rarara.

Mawaƙan da  su ka yi wa Rarara rakiya zuwa Birnin Kebbi sun haɗa da Kamilu Koko da Alhaji Garba Gashuwa da wasu.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top