by Naziru Dalha
Taura Mata suna da banbanci hakazalika maza. Babu wani abu da ake amfani dashi wajen gwajin namiji mai nagarta.
Wasu na duba irin ingantacciyar rayuwa ne inda wasu kuwa suna kallon rayuwa mai cike wadata.
Amma wasu matan da yawa sun amince da wadannan halayen ko abubuwan da suke matukar son a tattare da namiji.
1. Sanya annashuwa Duk mutumin da zai sa mace cikin annashuwa zai iya janye hankalinta tare da dasa soyayyarsa a zuciyarta.
Kowa na da bukatar abokin zama mai saka shi cikin farin ciki koda kuwa ana cikin halin jarabawa.
2. Saukin kai da kula Ba sai mutum ya tseratar da mutane yayin gobara bane za a kira shi da mai saukin kai a cikin jama'a ba.
Namiji mai saukin kai da kula na iya sanya mace ta fada son shi ba kadan ba. A lokutan da damuwa ta samu mace, tana bukatar namiji mai kula a tare da ita.
3. Gaskiya Babu mai son makaryaci. Gaskiya kuwa babbar nagarta ce a tattare da namiji. Namiji mai gaskiya shine wanda zai iya sanar dake gaskiyar lamari ba tare da cin amana ba.
Gaskiya da biyayya a hade suka.
4. Soyayyar gaskiya Namiji mai iya nuna wa mace soyayya a koyaushe yana iya tafiya da zuciyarta. Akwai hanyoyin bayyana soyayya masu tarin yawa. Budewa mace kofar gida ko ta mota, rike mata hannu yayin tsallake titi ko kuna shawagi.
Kananan abubuwa ne dai ke bayyana tsantsar soyayya.
5. Nuna wa mace ita ta musamman ce Mata da yawa na son namiji ya nuna musu sun kasance na musamman.
Yabawa mace kwalliya, girki ko wani kokari da tayi don birgeka na kara mata soyayyar namiji.
Duk namijin da ke nuna wa mace ita ta dabance na samun matsuguni mai girma a zuciyarta.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment