A baya munyi bayanin Daushiyar mace, wato Senior Babs. Ita Hajiya matane da ake iya samunsu cikin zaurawa da kuma yan mata. Sai dai sunyi yawa a cikin zaurawa. 
Matane da suke samun arzikinsu ko dai ta hanyar mutuwar mazajensu ko iyayensu. Sun fi maida hankali akan kasuwanci ba su cika yin aikin gwamnati ba. Irin wadannan matan ake kira Hajiya. Sugar Mummies a turance.
Ita kuwa Shashar mace da ake ce dasu YO Babs. Matane da ake samunsu cikin yan mata da kuma zaurawa. Yarane gagararru ko kuma marasa mafadi. Wanda wasunsu ko auren fari basu yi ba wasu sunyi basu zauna ba. Wasu kuwa rawankansu yasa mazansu suka hakura dasu.
Irin wadannan matan mafi yawansu ba 'ya'yan kowa bane, ma'ana yaran da suka fito daga gidan talakawa amma saboda kyausu ko wani basirar da suke dashi sai suke samun daukaka ta wannan hanyar harma su zama abun kwatance a cikin al'uma.

Darasin mu na gaba zamu kawo yanayin zaman aure da irin wadannan matan..

Tsangayar Malam


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top