Dr. Kadiri babbar likitar kwakwalwa ce da ke aiki da asibitin Pinnacle a matsayin shugabar asibitin

- Ta bayyana yadda jima'i ke cirewa mata damuwa tare da warkar dasu daga wasu cutukan kwakwalwa da suka hada da ciwon kai

- Ta yi bayanin yadda jima'i ke cire damuwa ga mata tare da kara musu kima, baya ga gyara jiki da yake yi Legit ta ruwaito.

A ranar Asabar ne wata likitan kwakwalwa mai suna Dr Maymunah Kadiri, ta shawarci matan aure da su yawaita jima'i da mazajensu don rage damuwa tare da samun farin ciki.

Kadiri, shugabar asibitin Pinnacle ta bada wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a garin Legas.


Kamar yadda ta ce, jima'i ba wai gyara jikin mace kawai yake ba, yana da matukar amfani ga lafiyar kwakwalwa.

"A matsayinmu na mata, akwai bukatar mazajenmu su zama aminanmu, matukar muna bukatar lafiyar kwakwalwa ingantacciya. Ilimi ne ya nuna cewa, matan da ke samun jima'i akai-akai basu cika samun damuwa ba idan aka danganta su da wadanda basu samu."


"Jima'i na da matukar amfani. Maganin matsanancin ciwon kai ne ga mata. Mace na fadawa damuwa matukar yawan jima'in da take samu ya ragu."

"Jima'i da yawa yana takar rawar gani wajen kara wa mace lafiyar kwakwalwa tare da ingantacciyar rayuwa."

Dr. Kadiri, ta kara da kira ga matan da ke da damuwa da su yawaita yin jima'i, lamarin na kara musu kima da lafiya.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top