Illolin Da Suke Tattare Da Auren Dole:
Auren dole akasar Hausa, aure ne da akeyiwa yarinya(budurwa) ba tare da tana so ba, wato atursasa mata auren wani wanda ba shi ne zabinta ba, kuma a mafi yawancin lokuta iyaye suna yiwa diyarsu auren dole ne ga wani mutum wanda shekarunsa suka jaa, kuma sau da yawa, auren dole haka yake kasancewa a tsakanin Hausawa.
haka kuma, akan baiwa mutum karamar yarinya ya aura, kodai saboda mai hannu da shuni ne, ko kuma saboda wani mukami da yake dashi, ko kuma saboda wani dalili na samin abin duniya, wasu kuma suna yiwa diyarsu auren dole ne ta hanyar hadin zumunci ko kuma kulla alaka tsakanin iyaye ko kuma abokai.
Ko shakka babu iyaye sunada rawar takawa mai yawan gaske wajen fitarwa da diyarsu mijin da zata aura, domin sun fita hange da sanin yakamata, kuma addini ya basu dama, kamar yadda addini ya nuna cewa biyayya ga iyaye wajibine, don haka nema Allah yace aljannar ‘ya ‘ya tana karkashin iyayensu.
A lokacin Manzon Allah anyi wani mutun da ake kira da suna Mughir wanda Allah ya jarrabe shi da tsananin son wata mata da ake kira da suna Barira, amma kuma cikin ikon Allah ita kuma duk duniya babu wanda bataso irinsa (Mugheer), har saida takai yana bin ta a hanya, yana kuka, yana rokonta, da ta soshi, amma ita kuma ta kekasa kasa. Wata rana sahabbai suka ga irin halin da mughir ke ciki, suka cewa manzon Allah shin baza kashiga cikin al’amarin Mughir da Barira ba, Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, da kansa yace hakika anjarrabi Mughir da soyayyar Barira.
Manzon Allah ya taka da kafarsa mai daraja, yaje wajen Barira da kansa Salallahu Alaihi Wasallam, ya ce yanzu Barira baza kiso Mughir ba! Ta ce ya Manzon Allah! kana bani umarni ne, ko kuma kana bani shawara, yace ina baki shawara ne salallahu Alaihi Wasallam, ta ce ya Manzon Allah bana sonsa, haka Manzon Allah ya taso yana mamakin irin yadda zuciyar Barira bata nutsu da Mughir ba duk kuwa da irin yadda yake nuna soyayya a gareta. Ya ‘yan uwana da auren dole yana da muhalli a musulunci da Manzon Allah ya umarci Barira ta auri Mughir sai dai baiyi hakan ba.
Wannan shi ya nuna mana cewa addinin Musulunci bai yarda da auren dole ba, domin da ana yi, da saboda yadda Manzon Allah ya tausayawa Mughir da ya umarce ta da ta aureshi amma haka ya bata cikakken ‘yancin ta salallahu alaihi wasallam.
Yaka mata iyaye su sani cewa ‘ya ‘ya suna da kimar da shariah tabasu wajen zabar mijin da zasu aura, kuma auren dole babu abin da yake haifarwa sai bacin tafarki, da kuma, dana sanin da batada amfani. Galibi auren dole ke sanya karuwanci da yawon banza, harma da wasan kwaikwayo da kananan yara mata suka tsunduma cikin harkar gadan gadan, wanda da zaka ji tabakinsu sai kaji dalilin auren dole da kuma mutuwar zuciya yasa su wannan harkar.
Ko shakka babu illolin da suke tattare da auren dole sun bayyana karara kamar wata daren sha biyar a wannan zamanin, kuma yaka mata iyaye ayi hattara. Sannan akwai wani al’amari muhimmi, shi ne tarbiyya, galibin iyaye musamman maza sunyi sakaci da al’amarin tarbiyyar ‘ya ‘yansu mata inda suka barta a hannun iyayensu mata, haka suma mazan ina ganin matukar iyaye sun baiwa diyarsu tarbiyya mai kyau babu yadda za’ayi su bata zabi ta kauce masa. Kuma sannan iyaye maza babban laifin yana kanmu domin galibi bamu fiya nunawa ‘ya ‘yanmu mata soyayya ba kamar yadda muke nunawa maza, wannan ce ta ke sanyawa da yawan ‘yan mata basu da kwarin gwiwa akan iyayensu maza, saboda suna ganin kamar babu su a cikin yadda ake dama al’amura, ba’a neman shawararsu ko jin ta bakinsu.
Zaka ga uba baitaba sayawa diyarsa kayan kwalliya ba, bai san ya ta ke da wannan janibi na larura ba, domin mata tamkar kayan Karau ne, dole sai ana kula da su kuma ana bibiyarsu, kai hattana ma irin audugar da mata ke anfani da ita wani uban bai sani ba yaya diyarsa take yi, ba’a neman shawararsu anmaidasu tamkar bayi ba ‘ya ‘ya ba. Don Allah amatsayinka na mahaifi taya ‘yarka zata fahimci kana kaunarta bayan baka kulawa da duk wani al-amari da ya shafeta ba. Amma matukar zaka kula da ita ka saya mata kayan kwalliya akai-akai, da audugar mata da janyo ta ajiki, da nuna mata muhimmancin da ta ke da shi a rayuwa, dole idan ka nuna mata hanya tabi ko da kuwa ya ci karo da muradinta, amma muddin ana samun akasin haka dole shegu suyi yawa acikin gari, da masu yawon ta zubar, da ‘yan daudu, da ‘yan gud ebini kai harma da barayi da kasha-kashe; kamar yadda wani mawakin Nijar ya ke cewa “ashe mata mu bayinsu ne, komai dansu muke”. Kuma wannan maganar tasa haka take, kusan duk wani fadi tashi da muke a rayuwa karshe wajen mata ya ke komawa, idan kuwa haka ne to bai kamata mu yi sakaci da wannan janibi ba.
Haka Kuma, suma a nasu bangaren, iya ye mata suna da tasu gudunmawar da suke badawa wajen sagewa ‘ya ‘yansu mata gwiwa, domin suma basu cika tattaunawa da ‘ya ‘yansu mata ba, suna jin matsalolinsu na rayuwa da kuma na zamantakewa, tare da basu shawarwari akan irin tunanins da kuma irin hukuncin da suke kokarin yankewa rayuwarsu, an maidasu kawai tamkar ‘yan aiki, ba su da wani amfani illa su yi wanke-wanke da shara da dora sanwa da yiwa yara wanka, dole iyaye mata su janyo su ajiki da nusar dasu yadda raywa take da nuna musu suna da muhimmanci a rayuwa, kamar yadda suma Iyaye maza wannan wajabci bai saraya akansu ba; da iyaye suna haka, da babu wasu da zakaji sun fito suna babatun ‘yancin mata wai andanne masu hakki. Kaji wai matan da suka kasa zaman aure, su ke son samowa na cikin gida ‘yanci da walwala da jin dadi, duk kuwa da cewar ana danne hakkokin mata da yawa a gidajen aure.
Sanin kowanne magidancine yanzu musamman wanda yake da mota yadda ‘yan mata ke rububinsa daga ka tsaya abakin titi sayan wani abu, sai kaga yarinya tazo ta dauka ko dan ita ka tsaya, anan ya kamata duk wani magidanci yayi karatun ta natsu shin wadan nan ‘yan mata wane dalili ya sanya su wannan harkar, shin da ‘yar kace ta ke wannan hali ya zakaji abin a ranka, akwai takaici kwarai da gaske ganin wadan nan yara mata da zaka ji ta bakinsu sai kaji auren dole za’a yimusu shi ne suka gudo, ko kuma ma anyi auren ta gudo. Allah ya shirya mana ‘ya ‘yanmu, kuma yabamu ikon yimasu adalci gwargwadon iko, sukuma Allah ya sanya tsoron sa azukatansu su fahimci cewa iyaye suna da matukar muhimmanci arayuwa.
Yasir Ramadan Gwale
© Sirrinrikemiji
Post a Comment