Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
Tsohuwar jaruma wadda ta dade ana damawa da ita a cikin masana'antar finafinai ta Kannywood Amina Abubakar ta bayyana masana'antar a yanzu da cewar waje ne da ya ke tattare da rashin tsafta idan aka kwatanta da yadda ake gudanar da harkar a shekarun farko na kafuwar ta.
Jarumar wadda ta shafe kusan shekaru 25 tana gudanar da harkar fim wanda ta fara tun ana wasan Dabe har zuwa Dirama a gidan talbijin na CTV, wanda a yanzu ake kira da ARTV, zuwa fim din Video har zuwa shirin kwana Casain na Arewa 24, ta bayyana hakan ne ga wakilin mu Mukhtar Yakubu a lokacin da su ke tattaunawa da ita dangane da halin da harkar fim ta samu kanta a ciki a yanzu.
Ta ci gaba da cewa " A lokacin baya harkar akwai taimakon juna da ganin girman na gaba, ta yadda ko furodusa ko Darakta idan akwai Wanda ya ke gaba da shi to ya na girmama shi ne, ba zai kalli kansa a matsayin Darakta ba.
Kuma duk lokacin da mu ka fita aiki za ka ga wajen zaman maza daban na mata daban, kuma Idan mace ta je da lullubi to har a gama aikin tana tare da abin ta, sannan babu maganar bambanci wajen abinci duk haduwa ake yi a abinci iri daya, wani lokacin ma matan da su ke wajen su ne za su dafa abincin.
Amma yanzu abubuwa duk sun canza babu wani mai girmama wani sai dai idan kai ake yayi sai a zo ana girmama ka ana kamun kafa da kai."
Ta kara da cewa 'Sam wannan Dabi' ar babu ita a lokacin da aka kafa harkar fim daga baya ne aka shigo da ita, wannan ya sa a yanzu rigingimu suka yi yawa a masana'antar aka kasa magance su, saboda babu mai ganin girman wani kowa da inda ya sa gaba."
Daga karshe ta yi kira ga 'yan fim da su dawo da kyawawan Dabi' un da aka san harkar da su tun farkon kafuwar ta, wannan kuma shi ne zai sa a samu ci gaban da ake bukata a masana'antar gaba daya, Inji ta.
Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya
©HausaLoaded
Post a Comment