Image ©Htrust


Allah wadaran naka ya lalace, Yariman Saudiyya ya sake gayyato wata futsararriya


Allah wadaran naka ya lalace, Yariman Saudiyya ya sake gayyato wata futsararriyar mawakiyar Najeriya domin sheke aya a wani wasan kalan kuwa.

Wata fitsararriyar mawakiya yar Najeriya, kuma diyar attajirin nan Femi Otedola, DJ Cuppy ta bayyana cewa za ta halarci kasar Saudiyya domin halartar bikin kalankuwa, inji rahoton The Cables.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne shahararriyar mawakiyar duniya, Nicki Minaj ta soke halartar zuwa kasar Saudiyya domin cashewa, inda ta danganta dalilin fasa halartar taron wakar ga tauye hakkokin mata da gwamnatin Saudiyya ta ke yi. musamman na kin amincewa da luwadi da madigo da kasar takeyi,


Image ©Htrust

Cuppy ta sanar da niyyarta na halartar taron ne a shafinta na kasar sadarwar zamani ta Twitter, inda tace: ‘A matsayina na mace mai aikin sarrafa wakoki watau DJ, ina alfahari da gayyatar da aka min zuwa kasar Saudi Arabia domin na yi abin da na iya.

Har yanzu babu wani da ya yi ma Cuppy barazana, ba kamar a lokacin da Nicki Minaj ta yi shirin zuwa Saudiyya ba, wanda tace ta janye zuwa Saudiyyan ne domin bayyana goyon bayanta ga hakkokin mata da kuma hakkokin kungiyoyin yan luwadi, madigo, da masu sauya surarsu.

waishin kuna ganin yakamata saudiyya ta dinga gayyatar irin wannan mata futsararru kasar anya wannan ba zubar da kimar musulunci bane a duniya?

Post a Comment

 
Top