Daga Zainab Umar

Tarihi ya nuna cewa, matan aure a lokacin Sahabban Manzon Allah (SAW) suna sana’a da kuma ayyuka. Tarihin ya tabbatar mana cewa a wannan lokacin wasu matan suna sana’a ne da saka da kuma kitso, wasu kuwa ‘yan kasuwa ne. Haka kuma wasu matan da su ake zuwa filayen daga domin kula da majinyata da kuma abin da ya yi kama da hakan.

Tabbas idan kuwa a wancan lokacin mata masu daraja da mukami a wajen Allah sun kasance da suna haka, ashe kuwa babu wata hujja da wata mace a wannan lokacin za ta zauna ba tare da yin wata sana’a ba, ko kuma aikin yi ba. Ganin yadda rayuwa musamman a wannan kasar take gagarar mai sana’a da aikin yi bare kuma wanda ba shi da abin yi.

A shekarun baya, mata ne ke neman gidan da za su huta idan suka yi aure, ma’ana suna cewa ba za su aure kowane irin namiji ba sai wanda yake da abin hannunsa wanda ba za su sha wahala ba a gidansa. Sai gashi abin yanzu ya juye su maza n yake neman auren matan da za su huta sabanin abin da yake faruwa a shekarun baya, mace ta ce sai mai gida da mota.

Ba wai don wannan dalilin ba ne kawai ya kamata ‘yan uwa mata musamman matan aure za su yi sana’a ko kuma ayyukan kamfani masu zaman kansu ko na gwamnati ba, a’a, idan muka duba, a lokutan baya, duk wata matsalar mace idan ya taso mata, mijinta ne yake dauka, ma’ana matsalar da ba dole ba ne sai ya taimaka kamar na zuwa bikin ‘yan uwa ko kawaye ko kuma makamantansu. Amma yanzu idan aka kasa kashi goma yana da matukar wuya a samu hudu da suke iya daukar dawainiyar matansu da bai zame masu dole su dauka ba.

Yana da matukar wuya a yi wata daya ba tare da wani hidima na kashe kudi ya taso wa mata ba, idan kuwa haka ne, abu mafi sauki wajen maigida da ita kanta uwargidan shi ne su samu wata sana’a ko kuma idan mai illimi ce ta yi wani aiki domin sauwakewa kanta da shi maigidan nata tare da taimaka masa da wasu abubuwa na yau da gobe na cikin gida da ‘ya’yansu da kuma biya wa kanta wasu bukatu nata.

Sana’a ga ‘ya mace musamman wanda take da aure, ba wai kawai ita zai taimakawa ba, har da mijinta kamar yadda na fada a baya da ‘yan uwanta da na mijinta da kuma al’ummar da take ciki, haka shi ma aikin yi wajen matan aure. Sai dai kuma abin mamaki shi ne yadda a wannan lokacin ya zama cewa, wasu matan sun zauna sai abin da miji ya yi masa, wasu kuwa har nuna rashin godiyarsu da kuma kyautawar maza suke nunawa da zarar sun nemi wata bukata a wajensu ba su samu ba, ba tare da yin la’akari da yawan kawo bukatan nan nasu ba akai-akai.

Haka su ma wasu mazan suna da kishin ganin matansu suna wata sana’ar da za a ce sun fi su samu koma suna samun wani abin da za su yi wa kansu bukatan da ba sai sun tamba yi mazan nasu ba. Haka wasu mazan duk karatun da mace ta yi ba za su barta ta yi wani aikin da za ta taimaka wa kanta da shi mijin da kuma al’umarta ba. Irin wadannan mazajen da dama sun taimaka wajen haddasa matsala da kansu a gidajnesu, domin wasu suna auran matan ne da alkawarin barinsu su yi aiki, amma da zarar mace ta shigo gida sai kuma su nuna cewa hakan ba zata sabu ba sai a su yi ta biyanta albashi ba tare da ta yi aiki a wani ma’aikata ba.

Wasu mazan kuwa, irin sana’ar da matan suke da sha’awar yi ne ba sa kauna, da hakan kuma ake samun tashin hankula da kuma rashin jituwa, wasu lokutanma da jawo sanadiyar mutuwar aure.

Da akwai sana’o’i da damar gaske wadanda matan za su iya yin su ba tare da sun fita daga gidajensu ba, haka kuma da ayyuka da dama da matan aure za su iya yin su wanda hankalin mazajensu zai zamanto a kwance. Babban bukata dai shi ne ma’aurata su zamanto sun gamsu da wata matsaya da suka yardar wa juna a kan duk wani aiki ko sana’a da mace za ta yi.

Tabbas sana’a’o’i irin su gyaran gashi, dinki da makamantansu sana’a’o’in da ba sai mace ta fita wajen yin su ba idan har mijin nata ba ya bubatar fitarta daga cikin gida. Haka kuma da akwai sana’a’o’i na zamani irin su rubuce-rubuce da kuma zane na komfuta, su ma sana’o’i ne da mace za ta iya yin su tana cikin dakinta kuma a biyo ta domin nemansu.

Misali, dukkan macen da ta iya sarrafa komfuta musamman wace ta kware wajen iya zane, tana iya shiryawa mata masu yin wani biki katin gayyata.

Haka kuma matan da suka iya tace finaifinai ma’ana “editing” suna iya yin wannan harkar da ‘yan uwansu mata a cikin gida, ko da kuwa finafinai ne na bukukuwan mata.

Kamar dai yadda na yi bayani a baya ne. Sana’o’in da damar gaske na hannu da kuma kasuwanci suna nan da dama wadanda duk kishin da namiji yake da shi zai iya barin mace ta yi su, sai dai kuma idan ita macen ce take da wata matsala ta daban.

Indan babbar matsala take shi ne game da aikin yin a matan aure, duk da yake a yanzu ana samun sauyi fiye da lokutan baya, inda maza da dama suke barin matansu yanzu su fita domin yin ayyuka a ma’aikatu da dama, sai dai kuma har yanzu da sauran rina a kaba, domin har yau din nan da akwai wasu mazan da sam ba su amince da matansu su fita aiki ba saboda wasu dalilai.

Babban abin da yakamata ‘yan uwa mata su lura da su su ne, duk namijin da ya barki kina aiki ko sana’a ko kasuwanci, ya barki ne ko dai domin ya aureki da wannan sharadin, ko kuma domin kema ki taimakawa kanki da ‘yan’yanki da kuma ‘yan uwanki, kuma zai ji matukar dadi idan har wannan taimakon zai iso gare shi, don haka yana da kyau da kuma muhimmanci ‘yan uwa mata su lura da wadannan dalilan. Ya kamata maza magidanta su fahimci cewa, a duk lokacin da ka bar matarka yin wani aikin da zai kawo mata kudaden shiga, ko kuma wani sana’a ko kasuwanci, tabbas wata rana za ka iya amfana da wannan aikin nata ko kuma sana’ar ko kasuwanci. Don haka ne nake kira ga mazaje masu tsaurin ra’ayi na hana matansu yin wadannan abubuwa, da su sake nazari saboda ci gabansu da na matansu da zuri’arsu da ma al’umma baki daya.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top