Daga Muhammad Usman Gashua
Maulana Shehu (r.t.a) ya fara da cewa : Assalamu alaikum masu sauraron mu, ina wannan maganane a matsayi na na Mu'kaddamin Tijjaniyya, na samu labari da bashi da dad'i, cewa Gobna Ganduje har yanzu yana neman yadawo da sarautar masarautu wadanda Hukuma (Kotu) ta ture, wato bangaren Shari'a, yace "yana so ya baiwa wakilai su sake bashi dama ya nada Masarautun da kotu ta ture", ina rokon Ganduje! don ALLAH ! dan ANNABI ! ya nema mana zaman lafiya a Nigeria, ba Kano kadai ba, domin dukkan mu 'Yan Tijjaniyyan Nigeria muna tare da Mai Martaba Sarkin Kano, muna tare da fadar Kano, abinda ya taba wadannan duka ya ta'ba mu gabaki daya, kuma bazamu kyale ba, ina jawo hankalin sa, ya janye maganan nan yanda kotu ta rushe ababen nan nasa, to ya hakura tunda an maida Kano kamar yadda take kamar Shekara dubu da wani abu, ya hakura abinda yafi kyau ya zauna lafiya da Mutane ya dena jawowa kansa mummunan addu'a, ya daina jawowa kansa gaba da Jama'a.
Shehu yaci gaba da cewa : Mu yan Tijjaniyya muna da yawa, a Nigeria, ba Nigeria kadai ba duk inda muke ma muna tare da fadar Kano, kuma fadar Kano ita ta kawo mana Shehu Ibrahim a Nigeria, da kuma Africa baki daya, ba zamu mance da alkairin da suka yi mana ba, saboda haka muna tare da su, bama tare da duk wanda yake gaba dasu, saboda haka muna jawo hankalin Gobna Ganduje yabar maganar yadda Kotu ta rushe ta mayar da Kano yadda take, ina jawo hankalin sa, kada ya jawo mana fitina da tashin hankali, da rashin zaman lafiya, mu yan Tijjaniyya baki daya, damu da Masoyan mu, muna tare da Sarkin Kano, muna tare da fadar Kano, duk abinda ya taba wurin nan ya taba mu, bazamu kyale ba, mu ko bamu da, karfi muna da Addu'a, saboda haka muna jan hankalin Ganduje ya janye wannan magana yabar Kano kamar yadda ya same ta, kamar yadda iyayen sa suka samu Kano, yabar ta haka.
Shehu ya kara da cewa : Nasara (Bature) yazo yayi shegentakar sa, shekara 60, bai taba birnin Kano yayi mata kacha-kacha kamar yadda Ganduje yayin nan ba, mulkin Soja yazo yabar Kano lafiya kalau kamar yadda aka same ta, amma ya kamata shima yayiwa kansa Wa'azi ya raba kansa da fitina da tashin hankali, yabar Kano yadda ALLAH yayi ta, yadda take shekara-da-shekaru, maganar cewa "za'a sake yin sarauta a farfasa Kano a wargaza Kano wannan mummunan shawara ne, ina jawo hankalin sa, yayiwa kansa 'kiyamul-laili' ya rufawa kansa asiri kar ya jawowa kansa tsinuwa dayawa a bakin Yan Tijjaniyya da addu'oi munana a wurin Yan Tijjaniyya, mu yan Tijjaniyya muna tare da sarkin Kano da fadar Kano, mu Yan Tijjaniyya duk inda muke, duk abinda ya taba mu, baza mu kyale ba.
kuma Kano tun zamanin 'Fodiyawa' suna cewa "Ab'arku ha Kano", wato kasar 'Fodiyawa' gaba daya, garin da yafi kowanne gari albarka inji Shehu Dan Fodiyo, da 'ya'yan sa su Mahamman Bello, da kannen sa su Abdullahi, gari mafi albarka shine Kano, Shehun mu kuma Shehu Ibrahim Inyass yace "Buwrika fi Kano madal ana'i" wato Kano ALLAH yayi mata albarka kullum da kullum, yana cewa "Karajtu min Kano wa qalbi min Kano, walimla wa ahbabi fi Kano sa Kano" wato "Ni na fita daga Kano, amma zuciya ta tana Kano, dan me? Saboda masoya na suna Kano, wato yana nufin duk jama'ar da yake saduwa dasu suna Kano, Masoyan sa na Kano saboda haka ina jawo hankalin ina nanatawa Ganduje nasiha ya ajiye maganar fitinar karkasa Kano, da farfasa Kano yabar Kano kamar yadda ya same ta, kamar yadda iyayen sa suka same sa.
Shehu yace : Yafi masa zaman lafiya ya kare aikin sa na Gobna yana cikin zaman lafiya, yafi masa ya kare yana tirka-tirka dashi ana ta tsine masa ana zagin sa, bakyau mutum yana nemawa kansa kyakkyawar makoma da kyakkyawar karshe baya nemawa kansa mummunar makoma, da mummunan karshe, taba fadar Kano, taba mu ne, da masoyan mu duka inda muke ba Nigeria kadai ba, duk inda muke (Aduniya), da fatan Gobna Ganduje yaji wannan shawara da na bashi ALLAH yasa yayi aiki da ita, yabar Kano ta zauna lafiya, kamar yadda yasame ta.
A karshe shehu yace : muna fatan masu hankali daga cikin mutanen Kano su matsa kusa dashi suyi masa wa'azi da nasiha akan abinda yasa agaba dinnan bashida kyau bazai masa kyau ba zai kawo masa bashi da kyau ALLAH ya kiyaye WANDA YAKE MAKA WANNAN NASIHA SUNAN SA DAHIRU USMAN BAUCHI DAGA BAUCHI YAKE, SALAMU ALAIKUM.
03/12/2019.
©HausaLoaded
Post a Comment