Yau shekara biyu kenan Gwamnatin jihar Kano a karkashin Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta shirya wa masu harkar fim wani taron sanin makamar aiki wanda a wancan lokacin aka shafe tsawon mako hudu ana koyar da su yadda za su gudanar da harkar su, kuma tsawon lokacin mutane 450 ne su ka samu horo.
Tun daga wancan lokacin ne 'yan fim din su ke jiran ranar da za a ba su takardar shaidar su, amma dai hakan ba ta samu, sai a wannan lokacin Gwamnati ta shirya tare da saka ranar 14 ga wannan wata na Disamba za a bayar da takardar shaidar wanda kuma aka shirya za a yi taron ne cikin wani gagarumin biki a gidan Gwamnatin Kano tare da Karrama wasu 'yan fim da su ka bayar da gudummawa ga harkar.
Kan haka ne mu ka nemi jin ta bakin shugaban Hukumar tace finafinai ta jihar Kano Malam Isma'ila Na' Abba Afakallah, domin irin shirin da su ka yi, inda ya fara da bayyana mana cewar.
"To daman babban abin da mu ka sa a gaba shi ne bai wa matasa ilimi domin su samu hanyar dogaro da kai, kuma Gwamnati ta yi nazari ta gano babbar matsalar harkar fim ita ce rashin ilimi, shi ya sa aka fitar da wannan tsarin na bai wa 'yan masana'antar ilimi, wanda aka dauki mutane 450 aka horas ta su a wancan zangon, kuma a yanzu ana so a Kara daukar wasu gida 500,domin a samar musu da horo, sannan daga cikin mutane 450 na baya Gwamna ya ce za a tantance a samar da wadanda za a fitar da su waje domin su kara ilimi."
Ya Kara da cewa" Dangane da shirin da aka yi kuma na ranar 14 ga wata, bayan an raba takardar shaida ga wadanda su ka samu horon da rana, kuma za a yi gagarumin biki da daddare, wato BON AWARD, wada za a bada Kambun Karramawa ga jarumi fittace da kuma jaruma fitacciya, domin karfafa musu a kan sana'ar su, kuma mu na sa ran manyan mutane za su halarta kamar Minista da sauran manyan jami`an Gwamnatin tarayya.
Don haka wannan muhimmin taro ne wanda za a iya cewa ba kamar irin wadanda aka saba shiryawa a baya ba, saboda da haka ina rokon jama'a da su ba da hadin kai domin ganin abubuwan da aka tsara sun tafi yadda su ka kamata.
Daga karshe ya yi godiya ga masu harkar fim bisa goyon bayan da su ke bayarwa, kuma su ci gaba da bada hadin kai domin samar wa da masana'antar abubuwan da za su rinka kawo mata ci gaba.
Haƙƙin Mallaka, Jaridar Dimokuraɗiyya
©HausaLoaded
Post a Comment