Maza Suna Aurenmu Ne Sabida Suyi Amfani Jikinmu Sai Su Sake Mu - Fati KK
A wata hira da aka yi da tsohuwar jaruma Fati KK ta bayyana cewa abinda maza ke bukata a jikin mace mai kyau irinta shine su aureta su gama jin dadinta su sake ta
Ta ce yanzu ita tsoron sake yin aure take yi, saboda tana kallon maza duka halinsu daya ne

Ta bayyana cewa ta fito daga wajen iyaye da suke da fahimta ga kuma ni’ima ta addinin Muslunci ita ce ta saka kullum take yiwa Allah godiya

Fati KK tsohuwar ‘yar wasan fina-finan Hausa ce ta Kannywood wacce bata bukatar muyi dogon labari game da ko wacece saboda sunan da tayi lokacin da take masana’antar. ‘Yar asalin garin Kontagora ce dake jihar Neja.

A lokacin da tauraruwar Fati ke haskawa kawai sai aka nemeta aka rasa abinda yasa masoyanta wasi-wasin inda ta shiga.

A wannan hirar da ta yi da Aliyu Askira wakilin jaridar Blueprint, ta yi bayani akan auren, da kuma dawowar ta harkar fina-finan Hausa.

Jaridar Blueprint: Menene sirrin wannan kyau din da kika kara?

Fati KK: Farko dai zan iya cewa ina farin ciki na samu iyaye wadanda suke da fahimtar rayuwa, da kuma addinin Musulunci, addinin da yake nuna mana cewa duk abinda ya faru da kai ka dauke shi a matsayin kaddara.

©Jaridar Blueprint

Post a Comment

 
Top