Yadda Kwadayin Abin Duniya Yake Jefa Matan Aure Shaye-shaye, Zina Da Kuma Madigo
Daga Real Fauziyya D. Suleiman
A iyakacin Saninmu tun daga yarinta kawo girma ko gyalan mace namijin da ba mjin ta ba bai isa ya taba ba balle jikinta balle har ya kai ga aika wani mummunan aikin da ita ba saboda kamun kai, domin ita mai daraja da kima ce, amma sabanin yanzu da macen ce da kanta ke kai kanta ga mazan, kuma macen aure.
Matuka hankalina ya tashi lokacin da na ji labarin mutuwar wani aure, da na tuntubi mijin don nasiha ya sanar da ni matar tasa bin maza da shaye-shaye har da bin mata ta ke yi don neman abun duniya, bayan bai gaza daidai karfinsa ba, lamarin ya girmame min matuka bayan da ya bani labarin komai, na jima da jin irin wannan labaran, don haka na kara bincike, na tarar da abun ya kazanta musamman ga wayayyun mata, kuma dalilin bin mazan na su da shaye-shaye.
Bai wuce don kwadayin abun duniya ba, wance na da kaza nima sai na yi, ko kuma irin salon nan na burge duniya nima ace na tara kaza, abun yana farawa yawanci tsakaninsu da mazan ta rokon katin waya sai tura hotuna na tsiraici sai haduwa, irin dai yadda waccen Matar auran ta dinga yawo hotal-hotal abun kyama, ko budurwa ce ta yi haka ta zama abar Allah wadarai balle ke da auranki.
Babban abun tashin hankalin yadda su ke kawo yaran da ba jinin mazajansu ba gidan, shi ya saka tarbiyyar ta ke kara lalacewa kullum.
To ki sani kafin ke an yi mata da suka yi tashe a samun duniya da abun duniya, ina irinsu Kugu zalla, irinsu ‘yar carascas da sauran matan da su ka yi duniyanci, sun gama babu komai sun kare a banza, kamar kuma waccen matar da ta kare a tozarce ta rasa mijinta da kimarta, don haka ki sani wallahi duk abun da zaki tara ta hanyar haram kararre ne, sannan ki je ki tadda fishin Allah bayan tozarcin duniya da rashin kwanciyar hankali. Wannan nasihar har mata marasa auran ma.
Ki sani duniya zancen banza ce, kiyi abun kirki da mijinki da ‘ya’yanki da danginki za su yi alfahari da ke duniya da lahira.
Mazan kuma da ke neman matan aure saboda wasu dalilai da bai kamata na fada anan ba, wallahi ku sani ba banza ku ka ci ba, matanku da ‘ya’yanku suma ba za su tsira ba, kuci gaba da neman matan wasu kuma za a nemi na ku, Allah ya shiryemu ya nisantamu daga aikata ba daidai ba amin.
The post Yadda Kwadayin Abin Duniya Yake Jefa Matan Aure Shaye-shaye, Zina Da Kuma Madigo appeared first on ArewaFresh.com™.
©Arewafresh
Post a Comment