Wasu hakimai 11 da suka fada arkashin sabbin masarautun da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kirkira sun halarci hawan Sallah na yammacin ranar Litinin a masarautar sarkin birnin Kano, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.

Majiyarmu ta samu asali daga legithausa, Sun halarci hawan na 'Daushe' ne sabann umarnin da gwamnatin Kano ta fitar a kan cewa kowanne hakimi ya halarci hawa Sallah a karkashin sabon sarkin masarautarsa.

Hakiman da suka kauracewa umarnin Ganduje tare da yin biyayya ga sarkin Kano, Sanusi II, sune; Madakin Kano; Yusuf Nabahani (hakimin Dawakin Tofa), Dan Amar; Aliyu Harazimi Umar (hakimin karamar hukumar Doguwa), Muhammad Aliyu (hakimin Garko), Makama; Sarki Ibrahim (hakimin Wudil), sarkin fulani; Ja'idinawa Buhari Muhammad (hakimin karamar hukumar Garin Malam, da Barde; Idris Bayero (hakimin karamar hukumar Bichi).

 Ragowar sune; Sarkin Bai; Adnan Mukhtar (hakimin karamar hukumar Danbatta), Yarima Lamido Abubakar (hakimin karamar hukumar Takai), Dan Isa; Kabiru Hashim (hakimin warawa), Dan Madami; Hamza Bayero (hakimin karamar hukumar Kiru) da Sarkin Dawaki Mai Tuta; Bello Abubakar (hakimin karamar hukumar Gabasawa).


 A wani jawabi da, Abba Anwar, kakakin gwamna Ganduje ya fitar ranar Lahadi, gwamnatin Kano ta bukaci Hakiman da su yi watsi da umarnin sarkin Kano na su zo birnin Kano domin gudanar da hawa tare da umartarsu da su gudanar da hawa a karkashin sabbin masarautunsu.

 Umarnin gwamnatin jihar ya saba wa sanarwar da fadar masarautar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta fitar, inda ta gayyaci dukkan hakiman jihar Kano da su halarci hawan Daushe, wanda aka saba yi kwana daya da Sallah.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top